Yanzu-yanzu: Dino Melaye ya shiga uku yayinda kotu tayi watsi da kararsa

Yanzu-yanzu: Dino Melaye ya shiga uku yayinda kotu tayi watsi da kararsa

Labarin da ke shigowa da duminsa na nuna cewa babban kotun tarayya dake birnin tarayya Abuja ta yi watsi da takardar karar da sanata Dino Melaye ya shigar cewa yan sanda su bar kofar gidansa kuma kada ku kamashi.

Dini Melaye ya kai kara kotu ne bayan jami'an hukumar yan sanda sun kai masa hari gida a makon da ya gabata kuma har yanzu ya ki fitowa.

A shari'ar da Alkalin ya yanke da safiyar Alhamis, Jastis N.E Maha, ya yi watsi da bukatar Melaye amma yace idan yanada kwakkwaran hujja ya gabatar.

Mun kawo muku rahoton cewa Rundunar 'yan sanda ta sake jibge wasu jami'anta 50 a gidan Sanata Dino Melaye dake Abuja. Wannan matakin kuwa ya biyo bayan yunkurin da majalisar dattijai ta yi na daukar mataki akan rundunar, na mamaye gidan Melaye tun ranar Juma'a.

Majalisar dattijai ta tabbatar da cewa matakin da zata dauka zai samar da 'yanci ga sanatan, wanda ke wakiltar mazabar Kogi ta Yamma a majalisar dattijan. Rahotanni sun bayyana cewa rundunar 'yan sandan na iya yin duk mai yiyuwa na kutsawa a gidan, don cafke sanatan.

Rundunar 'yan sanda ta bayyana Melaye a matsayin wanda take nema ruwa a jallo, bisa zarginsa da harbin wani jami'inta, Sajen Danjuma Saliu da ke aiki a rundunar yan sandan sintiri ta 37, a lokacin da yake bakin aiki, kan titin Aiyetoro-Gbede-Mopa, a jihar Kogi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel