Ba a kulle hanyar Maiduguri-Monguno ba – Rundunar soji

Ba a kulle hanyar Maiduguri-Monguno ba – Rundunar soji

- Rundunar sojin Najeriya ta karyata wasu labarai da ke yawo a shafukan zumunta cewa an rufe hanyar da ke sada Maiduguri da Manguni a jihar Borno

- Kakakin rundunar ya bayyana rahoton a matsayin kanzon kurege

Rundunar sojin Najeriya ta karyata wasu labarai da ke yawo a shafukan zumunta cewa an rufe hanyar da ke sada Maiduguri da Manguni a jihar Borno.

Mataimakin kakakin rundunar Operation Lafiya Dole, Onyema Nwachukwu ya bayyana rahoton a matsayin kanzon kurege.

Ba a kulle hanyar Maiduguri-Monguno ba – Rundunar soji

Ba a kulle hanyar Maiduguri-Monguno ba – Rundunar soji
Source: Depositphotos

Hukumar sojin ta ce sabanin hasashen, hanyar Maiduguri - Monguno na nan a bude ta yadda dukkanin matafiya da suka bi ka’idan doka za su iya wucewa.

Rundunar sun mamaye hanyar ne domin yin sintiri yayinda suke aikin kakkabe yan ta’addan Boko Haram a hanyar Baga.

Don haka ta nemi jama’a da su yi watsi da rade-radin.

KU KARANTA KUMA: Za a hukunta duk wanda aka kama yana amsar cin hanci - Buhari

A baya mun ji cewa Rundunar sojin Najeriya ta karyata rahotannin cewa yan ta’addan Boko Haram sun kwace garuruwa shida a jihar Borno.

Daraktan labarai na rundunar, Birgediya Janar Sani Usman, ya karyata rahoton a wani sako da ya aikewa Channels TV a ranar Litinin.

Ya ce lallai rahoton kwace garuruwan guda shida da aka ce yan ta’addan sun yi bata ne.

Sakon Birgediya Janar Usman na zuwa ne kwanaki kada bayan an kawo cewa ayyukan Boko Haram na karuwa a Baga da kuma rahoton cewa yan ta’addan sun kwace garuruwa shida a karamar hukumar Kukawa da ke Borno.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel