Dalilin da ya sa ba a binne Shagari a Hubbare ba

Dalilin da ya sa ba a binne Shagari a Hubbare ba

Iyalan tsohon shugaban kasar Najeriya, Alhaji Shehu Shagari yi Karin haske akan dalilin da yasa aka binne marigayin a gidansa maimakon Hubbaren Shehu, sun bayyana cewa marigayin da kansa ne ya nuna inda za a binne shi idan ta Allah ta kasance akansa.

Iyalan marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya, Alhaji Shehu Shagari sun bayyana cewa marigayin da kansa ne ya nuna inda za a binne shi idan Allah ya karbi ransa.

Babban dansa Alhaji Bala Shehu Shagari wanda shi ne Sarkin Shagari ne ya bayyana hakan a matsayin wasiyar da mahaifinsa ya bari.

Dalilin da ya sa ba a binne Shagari a Hubbare ba

Dalilin da ya sa ba a binne Shagari a Hubbare ba
Source: UGC

Marigayi Shehu Shagari ya rasu ne a ranar Juma'a a 28 ga watan Disamba a wani asibiti da ke babban birnin tarayya Abuja yana da shekaru 93.

An binne shi ne kuma a wani kangon daki da ke wani sashen na gidansa da ke garin Shagari ranar Assabar.

Mutane da dama sun yi tsammanin za a binne shi ne a Hubbaren Shehu inda kabarin Sheikh Usmanu Danfodiyo da na yawancin sarakunan daular Usmaniyya suke.

KU KARANTA KUMA: CUPP ta bukaci ayi ma Buhari, Atiku gwajin hankali gabannin zaben 2019

A cewar babban dan nasa, marigayin ya yi wannan wasiyyar ne fiye da shekaru 10 kafin rasuwarsa da yammacin ranar Juma'a.

"Mai alfarma Sarkin Musulmi ya taya mana cewa muna iya kai shi Hubbare amma sai na fada masa cewa shi ga inda ya ce a binne shi; kuma a Musulunce wasiya na gaba ga duk wani abu" in ji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel