Shehu Sani ya mayar da martani kan mukamin da aka ba Dangote a kwamitin kamfen din Buhari

Shehu Sani ya mayar da martani kan mukamin da aka ba Dangote a kwamitin kamfen din Buhari

- Sanatan yace kada a dauki nade-naden jam’iyyar mai mulki da wani muhianci kamfen din Buhari

-Sanatan yace kada a dauki nade-naden jam’iyyar mai mulki da wani muhianci

- Ya kuma shawarci Dangote da ya mayar da hankali ga kasuwancinsa maimakon shiga APC

Sanata mai akiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya ya mai d martani ga labarin da aka saki dazu game da nadin shahararren dan kasuwan Najeriya, Aliko Dangote, da shahararren attajiri, Femi Otedola, da kuma Tinubu cikin kwamitin kamfen din shugaban kasa da jam’iyya All Progressives Congress (APC) tayi.

Shehu Sani ya mayar da martani kan mukamin da aka ba Dangote a kwamitin kamfen din Buhari
Shehu Sani ya mayar da martani kan mukamin da aka ba Dangote a kwamitin kamfen din Buhari
Asali: UGC

Sani a wani rubutu da ya wallafa a shafin twitter a ranar Juma’a, 28 ga watan Disamba yace kada a dauki nade-naden jam’iyyar mai mulki da wani muhianci.

Sanatan ya kua shawarci Danote da ya ci gaba da kasuwancn gabansa maimakon shiga jam’iyyar mai mulki a gabannin zaben shugaban kasa na 2019.

Ga abunda ya wallafa a shafin nasa:

KU KARANTA KUMA: Shehu Sani yi martani bayan ikirarin cewa iyalan Buhari na da hannun jari a kamfanoni 2

A baya mn ji cewa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta ba babban jigon jam’iyyar na kasa, Bola Tinubu, da kuma babban attajirin dan kasuwan nan kuma biloniya Aliko Dangote mukamai a kungiyar kamfe din dan takararta na shugaban kasa a zaben 2019.

Legit.ng ta tattaro cewa an saki cikakken sunayen mambobin kwamitin shugaban kasar a ranar Juma’a, 28 ga watan Disamba daga hannun babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Femi Adesina.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel