Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira jihar Akwa Ibom

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira jihar Akwa Ibom

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira jihar Akwa Ibom domin kaddamar da yakin neman zaben kujeran shugabancin kasan Najeriya a zaben 2019 na yankin kudu maso kudancin kasar a yau Juma'a, 28 ga watan Disamba, 2019.

Za'a gudanar da zaben shugaban kasa a watan Fabrairu 2018.

Shugaban kasan ya isa jihar ne misalin karfe 4 na yamma tare da wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress APC.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira jihar Akwa Ibom
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira jihar Akwa Ibom
Asali: Facebook

Daga cikin wadanda suke hallare a taron sune babban jigon APC, Asiwaju Bola Tinubu; shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole; ministan sufuri kuma diraktan kamfen Buhari, Rotimi Amaechi.

Daga cikin gwamnonin da suke taron sune gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i; gwamnan jihar Ogun, Ibikunle amosun; gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu; gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; gwamnan jihar Oyo, Ajibola Ajimobi.

Sauran sune mataimakin jihar Kano, Ali Gawuna; mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Silas Ali Agara; gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira jihar Akwa Ibom
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira jihar Akwa Ibom
Asali: Facebook

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira jihar Akwa Ibom
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira jihar Akwa Ibom
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel