Hutun Kirsimeti: Ma’aikata sun yi kaura a majalisar dokokin tarayya duk da cewar hutu ya kare

Hutun Kirsimeti: Ma’aikata sun yi kaura a majalisar dokokin tarayya duk da cewar hutu ya kare

- Ma’aikata da dama a majalisar dokokin kasar sun ki zuwa wajen aiki duk da cewar hutun kwana biyu da gwamnatin tarayya ta bayar domin bikin Kirsimeti ya kare

- Gwamnati dai ta bayyana ranakun 25 da 26 ga watan Disamba a matsayin hutu domin bikin Kirsimeti

- Cikin tarin ma’aikatan majalisar yan kadan ne suka je aiki suma kuma sun tashi tun kafin lokaci yayi

Ma’aikata da dama a majalisar dokokin kasar a ranar Alhamis, 27 ga watan Disamba sun ki zuwa wajen aiki duk da cewar hutun kwana biyu da gwamnatin tarayya ta bayar domin bikin Kirsimeti ya kare.

Gwamnati dai ta bayyana ranakun 25 da 26 ga watan Disamba a matsayin hutu domin bikin Kirsimeti yayinda 1 ga watan Janairu, 2019 zai zama hutun sabuwar shekara.

Ana sanya ran ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu su koma bakin aiki a ranar Alhamis kasancewar sa 27 ga watan Disamba.

Hutun Kirsimeti: Ma’aikata sun yi kaura a majalisar dokokin tarayya duk da cewar hutu ya kare

Hutun Kirsimeti: Ma’aikata sun yi kaura a majalisar dokokin tarayya duk da cewar hutu ya kare
Source: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa an gano wasu jami’an yan sanda da na hukumar hana afkuwar hatsarurruka na ta gudanar da ayyukansu.

Akwai sauran wasu ya tsirarun ma’aikata kamar masu goge-goge, ma’aikatan banki, yan jaridu da sauransi da aka gano a harabar majalisar dokokin kasar.

KU KARANTA KUMA: Yari ya kwace min hakkokina – Mataimakin gwamna

An lura cewa hatta da ma’aikata kadan din da suka je aiki sun tashin kafin lokacin tashin yayi.

Sanatoci 109 da yan majalisar wakilai 360 dama hutun wata daya suka tafi inda za su dawo a ranar 16 ga watan Janairu.

Wani ma’aikaci yace mafi akasarin ma’aikatan basa Abuja sun yi tafiya kuma ba lallai ne su dawo ba sai a wata Janairu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel