Wata mata ta datse al'aurar makwabcinta da ya dade yana cin zarafinta

Wata mata ta datse al'aurar makwabcinta da ya dade yana cin zarafinta

- Wata mace da datse azzakarin wani makwabcinta ya dade yana cin zarafinta

- Matar mai shekaru 42 ta nemi taimakon wasu maza biyu suka yiwa makwabcinta duka kuma ta datse azzakarinsa

- A halin yanzu mutumin yana gadon asibiti cikin mawuyancin hali inda likitoci ke kokarin ceto ransa

Wata mace mai matsakaicin shekaru a kasar Indiya datse azzakarin wani mutum da ya rika fitinar ta babu dalili inda aka garzaya da shi asibiti domin ceto rayuwarsa kamar yadda 'yan sanda suka ce a ranar Alhamis.

Matan da ake zargi ta umurci wasu maza biyu ne a ranar Talata su yiwa matashin mai shekaru 25 dabara su kai shi wani unguwa da babu mutane sosai a bayan garin Mumbai inda suka taru su uku suka masa dukka.

Wata mata ta datse al'aurar makwabcinta da ya dade yana cin zarafinta
Wata mata ta datse al'aurar makwabcinta da ya dade yana cin zarafinta
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya lissafo dalilai 3 da yasa manyan Arewa su kayi gum a kan yawaitar kashe-kashe a yankin

Sannan mata tayi amfani da wuka ta datse azzakarinsa, inji 'yan sanda.

Matar mai shekaru 42 ta fadawa 'yan sanda cewa mutumin makwabcin ta ne kuma ya dade yana cin zarafinsa.

"Hakan yasa ta dauki matakin koya masa darasi", kamar yadda wani dan sanda ya shaidawa Reuters.

Amma daga bisani ta lura cewa zai iya mutuwa hakan yasa ta garzaya da shi asibiti.

An gano wuka da azzakarinsa da ta datse, in 'yan sanda.

"Yana nan cikin muwuyacin hali a asibiti," a cewar wani likita da ke asibitin.

Matar da maza biyun da suka taimaka mata wajen aikata laifin suna hannun 'yan sanda a yayin da ake cigaba da bincike.

Cin zarafin mata da fyade laifi ne da ke kara yaduwa a kasar Indiya a cikin 'yan shekarun nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel