Mun riga mun ci karfin ‘Yan ta’addan Boko Haram – inji Janar Buratai

Mun riga mun ci karfin ‘Yan ta’addan Boko Haram – inji Janar Buratai

Duk da munanan hare-haren da ‘Yan ta’addan Boko Haram su ke kai wa, shugaban sojojin kasa na Najeriya, Laftana Janar Tukur Buratai yana cigaba da ikirarin cewa sojoji sun yi galaba a kan ‘yan ta’ddan.

Mun riga mun ci karfin ‘Yan ta’addan Boko Haram – inji Janar Buratai

Laftana Janar Buratai yace ta karewa 'Yan ta'addan Boko Haram
Source: UGC

A sakon sa na kirismeti da ya aikawa sojojin Najeriya da ke fagen daga a Yankin Aeewa maso gabas, shugaban hafsun soja na kasar, Tukur Buratai, ya bayyana cewa tuni an gama lallasa ‘yan Boko Haram, sai dai abin da ba za a rasa ba.

Janar Tukur Buratai ya hakikance da cewa sun ci karfin ‘yan ta’addan Boko Haram. Buratai ya kara da cewa Boko Haram kananun tsagerori ne kurum da ke kokarin juya hankalin jama’a domin nuna cewa har gobe su na da wani karfi.

KU KARANTA: An nemi a sauke hafsun Sojojin Najeriya bayan an hallaka Jami'an tsaro

Tukur Yusuf Buratai ya zargi ‘yan ta’addan da amfani da furofanda domin yi wa Duniya barazana, amma yace a hakikanin gaskiya, an samu nasara a kan ‘yan Boko Haram. Janar Buratai ya kuma nemi sojojin su kakkabe ragowar ‘yan ta’addan.

Babban sojan kasar ya tunawa rundunar sa cewa an san sojojin Najeriya da tarihi a ko ina a Duniya, sannan kuma yace sojin na sa sun fi ‘yan ta’addan sanin yaki da kuma samun isasshen horaswa, don haka ya nemi su kara azama a filin daga.

A sakon sa na kirismeti da shirin shiga sabuwar shekara, hafsun sojan ya nemi sojojin da cewa su kara kaimi ka da su karaya da irin manakisar da Boko Haram su ke yi na yunkurin sanyawa sojojin kasar dar-dar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel