Danjuma-da-Danjummai: 'Yan shi'a sun taya kiristoci bikin kirisimeti a cocin Kaduna

Danjuma-da-Danjummai: 'Yan shi'a sun taya kiristoci bikin kirisimeti a cocin Kaduna

A lokacin bukukuwan Kirsimeti da Kiristoci ke gudanarwa a fadin duniya, almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky da akafi sani da 'yan shi'a sun yi amfani da wannan damar wajen kaiwa Kiristoci ziyarar a cocin ECWA Good News dake Kaduna.

Shugaban Cocin Rabaran Istifanus Isa ya gabatar da wakilin 'yan’uwa a wurin wato Dk. Shu'aibu Musa, inda ya yi jawabi na taya murna da kuma gabatar musu da saƙon Harka Musulunci, da kuma matsayin Kiristoci a wurin mabiya Harkar da sauransu.

Danjuma-da-Danjummai: 'Yan shi'a sun taya kiristoci bikin kirisimeti a cocin Kaduna

Danjuma-da-Danjummai: 'Yan shi'a sun taya kiristoci bikin kirisimeti a cocin Kaduna
Source: UGC

KU KARANTA: Atiku ya kada Buhari a wani zaben gwaji

Bayan nan ne, aka gabatar da waƙoƙi daga Ammar Ɗan Tinka da Muhammad Baƙir.

Mahalarta Cocin, sun nuna jin dadinsu sannan sun ce; sun ƙara fahimtar Musulunci ba addinin ta'addanci bane, addini ne na zaman lafiya.

Sun kuma nuna gamsuwarsu da yadda ba a kyamace su har aka zo muhallinsu domin taya su murna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel