Kisan mutane uku: Dan majalisar wakilai daga Kano ya shiga tsaka mai wuya

Kisan mutane uku: Dan majalisar wakilai daga Kano ya shiga tsaka mai wuya

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano na binciken mamba a majalisar wakilai mai wakiltar mazabun Wudil da Garko, Muhammad Ali Wudil, a kan kisan wasu mutane uku a karamar hukumar Rano.

A kalla mutane uku ne suka mutu yayin kaddamar da yakin zaben jam'iyyar APC a shiyyar Kano ta Kudu da aka yi a garin Rano.

A wani jawabi da hukumar 'yan sanda ta fitar a ranar Alhamis ta bakin kakakinta na jihar Kano, Magaji Musa Majiya, ta ce tana da hujjoji masu karfi a kan dan majalisar kuma nan ba da dadewa ba zasu gayyace shi.

A cewar Majiya, rundunar 'yan sanda ta umarci dan majalisar da kar ya halarci taron saboda wasu dalilai na tsaro da hukumar ke da su a kansa, amma ya yi watsi da umarnin.

Kisan mutane uku: Dan majalisar wakilai daga Kano ya shiga tsaka mai wuya

Muhammad Ali Wudil
Source: Facebook

Ya kara da cewar hukumar 'yan sanda na da shaidar cewar dan majalisar ya halarci taron da gungun 'yan daba da suka hallaka mutane yayin taron.

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar daya daga cikin mambobin majalisar wakilai 'yan jam'iyyar PDP ya bayyana cewar sun yiwa shugaba Buhari ihu ne domin nuna rashin jin dadinsu bisa yadda gwamnatin tarayya ta gaza yin aiki da kasafin kudin shekarar 2018 kamar yadda ta gabatar.

A ranar Laraba ne wasu mambobin majalisar wakilai suka yiwa shugaba Buhari ihu yayin da ya isa zauren majalisar domin gabatar da kasafin kudin shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Dalla-Dalla: Tsoho dan shekaru 85 da aka kama da zuciyar mutum ya yi bayani

Da shigar Shugaba Buhari zauren majalisar sai wasu mambobi suka kaure da ihun "noooo", "noooo" tare da yin ihun "karyane", "karyane" lokacin da Buhari ya fara zayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu.

Da yake ganawa da manema labarai bayan kammala gabatar da kasafin, shugaban wata kungiyar 'yan majalisar tarayya Jam'iyyar PDP, Chukwuma Onyema, ya bayyana rashin jin dadin 'yan majalisar a kan yadda bangaren zartarwa ke nuna son a kai wajen zabar aiyukan da zata kaddamar daga cikin wadanda ta gabatar a kasafinta na shekarar 2018.

Kazalika, ya bayyana cewar hatta yajin aikin da ma'aikatan majalisar ke yi na da alaka da rashin kaddamar da kasafin kudin shekarar 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel