APC ta yi martani kan caccakar Buhari a zauren Majalisa

APC ta yi martani kan caccakar Buhari a zauren Majalisa

Mun samu cewa, jiga-jigan jam'iyyar PDP na majalisar wakilan kasar nan, sun yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari wankin babban bargo dangane da kasafin kudin kasar nan da ya gabatar jiya Laraba a zauren Majalisar tarayya.

A ranar Laraba da ta gabata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya gabatar da kasafin kudin shekarar badi na N8.83tr a zauren majalisar dokokin kasar dake garin Abuja.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, wasu 'yan majalisar sun rinka ihu domin nuna adawa dangane da wasu bayanai na shugaban, yayin da wasu suka rinka sowa domin nuna goyon baya a gare sa.

'Yan Majalisar na jam'iyyar adawa ta PDP, sun bayyana kasafin kudin da shugaba Buhari ya gabata a matsayin shagulatan bangaro da ba bu wata mamora da za ya haifar ta ci gaban kasar nan.

APC ta yi martani kan caccakar Buhari a zauren Majalisa

APC ta yi martani kan caccakar Buhari a zauren Majalisa
Source: UGC

Honarabul Chukwuma Onyema, jigo na jam'iyyar PDP, kuma mataimakin shugaban majalisa marasa rinjaye a majalisar wakilai, ya ce gwamnatin APC kamar kullum za ta ci gaba da yin bankaura wajen tabbatar da duk wani tsare-tsare da tanadi na kasafin kudin kasar.

Ya ke cewa, soki burutsu da gwamnatin APC ta saba gindayawa cikin kasafin kasa shine ummul aba isi na mafi akasarin sabani a tsakanin majalisar tarayya da kuma fadar shugaban kasa.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wasu jiga-jigan 'yan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya kuma makusantan shugaban kasar sun bayyana rashin jin dadinsu game da ihun da aka yi wa Shugaba Buhari yayin gabatar da kasafin kudin 2019. Sun sha alwashin ramawa Kura aniyyar ta.

KARANTA KUMA: Mataimakin Shugaban kasa ya jagorancin Zaman Majalisar Zantarwa

Cikin wata sanarwa da sanadin babban sakataren hulda da al'umma na jam'iyyar, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana cewa, 'yan majalisar PDP sun kunyatar da kawunansu da kuma Najjeriya baki daya a idon duniya, baya ga rashin kishin kasa da suka tabbatar da ta mamaye zukatan su.

Mallam Lanre ya kara da cewa, 'yan Majalisar PDP sun shaidawa duniya akidar su ta son zuciya da kuma irin rashin jagoranci na gari na shugabannin majalisar, Abubakar Bukola Saraki da kuma Yakubu, da adawar siyasa ta rufe masu idanu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel