Karon farko: Buhari yayi magana game da yajin aikin kungiyar ASUU

Karon farko: Buhari yayi magana game da yajin aikin kungiyar ASUU

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari yayi magana game da yajin aikin da a halin yanzu malaman jami'o'in Najeriya ke cikin yi inda ya roke su da su duba halin da 'ya'yan al'ummar kasar suke su janye su koma bakin aikin su.

Shugaban kasar wanda mataimakin babban Sakataren hukumar dake da alhakin kula da jami'o'in kasar wata National University Commission ya wakilta a wajen bikin yaye daliban jami'ar Tarayya dake a garin Ebonyi.

Karon farko: Buhari yayi magana game da yajin aikin kungiyar ASUU

Karon farko: Buhari yayi magana game da yajin aikin kungiyar ASUU
Source: Twitter

Idan mai karatu bai manta ba dai mun ji cewa an tashi baram-baram a taron tattauna mafita tsakanin shugabannin kungiyar malaman jami'o'i na Najeriya watau Academic Staff Union of Universities (ASUU) a turance da kuma jami'an gwamnati domin tattaunawa akan yajin aikin da yanzu haka suke yi.

Majiyar mu dai ta bayyana mana cewa an ga shugabannin kungiyar sun fito daga dakin taron da suke cikin yi da jami'an gwamnatin a ma'aikatar ilimi ba tare da yiwa 'yan jarida bayani ba sannan kuma suka shige motocin su suka tafi.

Kamar yadda muka samu, shugaban kungiyar ta Academic Staff Union of Universities (ASUU) Biodun Ogunyemi ne ya jagoranci shugabannin kungiyar wadanda aka gani a ma'aikatar Ilimi ta gwamnatin tarayya a garin Abuja tun wajen karfe 5 na yamma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Online view pixel