'Kakkabe katobarar da PDP tayi a Najeriya ba karamin aiki ne ba ga Buhari'
Daya daga cikin tsaffin gwamnonin Najeriya daga jihar Enugu Sullivian Chime ya bayyana cewa gyaran Najeriya fa da shugaba Buhari ya fara ba zai yiwu ba cikin dan kankanen lokaci kamar adda jama'a ke tunani.
Tsohon gwamnan dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake fira da wakilin majiyar mu a gidan sa dake a garin Enugu, babban birnin jihar.

Asali: Depositphotos
KU KARANTA: EFCC tayi babban kamu a hukumar INEC
Legit.ng Hausa ta samu cikin firar cewa tsohon gwamnan wanda ya koma APC daga PDP a 'yan kwanakin nan, ya zayyana wasu ayyukan alherin da gwamnatin ta shugaba Buhari ke shimfidawa kamar su hanyoyi da sauran su da yace a da basu samu ba.
A wani labarin kuma, Wani bankin kananan masana'antu watau Microfinance Bank a turance dake a kan titin Bassey Duke, garin Kalaba na jihar Kuros Ribas ya gamu da babban cikasa biyo bayan wasu barayin da suka dirar masa tare da sace makudan kudaden kwastomomi.
Kamar yadda muka samu, barayin kusan su biyar ne suka kai harin a bankin bayan sun ajiye motocin su a waje da kusan karfe 3 na ranar Alhamis din da ta gabata kafin daga bisani su kusa kansu cikin bankin da tsiya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng