Labari mai dadi: Majalisar dattawa ta yi wa nakasasu gata
Rahotanni sun kawo cewa majalisar dokokin kasar ta aiwatar da wata doka da ta yi gyara a kai na matsalar nuna wariya ga masu larurar nakasa a fadin kasar.
Majalisar dattawan ta dauki wannan mataki ne bayan ta amshi wani rahoto daga kwamitin ta, wanda ya yi duba tare da nazarin kudurin dokar.
Shugaban kwamitin, Sanata Kabiru Marafa, ya bayyana wa majiyarmu ta BBC cewa dokar ta kunshi abubuwan da suka shafi lamuran rayukan dan adam, kuma sai da suka nazarci bangarori da dama kafin kafa ta.
Ya ce akwai lamura da yawa da aka duba da kuma wasu tanade-tanade da suka shafi 'yancin walwala da asibiti da gine-gine don ganin cewa masu irin wannan larura sun samu sauki a rayuwarsu.

Asali: Depositphotos
Sanata Marafa ya ce wannan doka za ta kawo karshen duk wani kalubale da masu nakasa ke fuskanta kamar wariya a wurin samun aiki.
Ya kara jadadda cewa sai da suka tuntubi kasashe da dama kafin zartar da dokar, inda suka nemi shawarwarin hanyoyin tabbatuwar ta a cikin nasara.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan majalisar wakilai 2 sun sake barin APC
Sanatan ya kuma kara da cewa babu aikin da zai gagari mai nakassa, abin da ake bukata kawai shi ne duba abin da ya dace da shi ba tare da ya zama kalubali ta kowanne fanin rayuwa ba.
Yanzu dai majalisar na jiran sa hannun bangaren zartarwa kafin dokar ta soma aiki a fadin Najeriya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng