Babu siɗiɗi babu saɗaɗa: Yan bindiga sun bude ma jama’a wuta, sun kashe 2

Babu siɗiɗi babu saɗaɗa: Yan bindiga sun bude ma jama’a wuta, sun kashe 2

Wasu tagwayen yan bindiga sun bude ma jama’a wuta, inda suka halaka mutane biyu tare da raunata jama’a da dama a daidai titin Waterline dake cikin garin Fatakwal, babban birnin jahar Ribas, inji rahoton jaridar Daily trust.

Majiyar Legit.com ta ruwaito lamarin ya faru ne da yammacin Laraba 21 ga watan Nuwamba, a lokacin da yan bindigan suka kutsa kai da baburan nasu cikin jama’a, suka fara harbin mai kan uwa da wabi a mahadar tituna ta Waterline.

KU KARANTA: Dandalin Kannywood: Daraktan daya shirya gadar zare, gagare, sangaya ya rasu

Wani shaidan gani da ido ya bayyana ma majiyarmu cewa suna tsaitsaye akan titin ne sai kawai suka fara jin karar harbi ta ko ina, nan da nan duk suka kwakkwanta don gudun kada alburushi ya samesu, anan take mutum daya ya mutu, daya kuma yam utu a hanyar zuwa Asibiti.

“Muna tsatstsaye a wurin duk jama’a anyi cirko cirko, kawai sai muka fara jin karan harbe harbe, daga nan sai masu gudu suka ranta ana kare, mu kuma muka kwanta a kasa, a garin gudun ne yan bindigan suka kashe mutane biyu.” Inji shi.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Ribas, Nnamdi Omoni ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai yace rahoton da suka samu ya bayyana cewa mutum daya ne yan bindigan suka kashe, amma a cewarsa mutum daya kuma ya samu munanan rauni.

A wani laabrin kuma wasu miyagun mutane sun yi awon gaba da wani karamin yaro mai shekaru bakwai, Monday Ajeh, daga gidansu dake kauyen Agaza ta cikin karamar hukumar Keana a jahar Nassarawa, inda suka kwakule masa idanu.

Mahaifin yaron mai suna Agadi Ajeh mai shekaru 47 ya bayyana mana yadda tsautsayi ya hau kan yaronsa Monday, inda yace lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, yayin da ya kwanta barci tare da iyalinsa da misalin karfe 1 na dare.

Suna cikin barci ne sai suka ji ihun yaron nasu yana neman taimako, amma fitarsa keda wuya don ganin halin sai ya fahimci an yi garkuwa da yaron, nan take suka tashi gungun matasa don nemo yaron, bayan wani dan lokaci suka gano shi kwance jina jina an kwakule masa ido.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel