Dama can APC bata yiwa 'yan Nigeria alkawarin gyara kasar a cikin shekaru 4 ba - Fashola

Dama can APC bata yiwa 'yan Nigeria alkawarin gyara kasar a cikin shekaru 4 ba - Fashola

- Mr Babatunde Raji Fashola, ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari bata taba cewa zata gyara kasar a cikin shekaru 4 ba, a lokacin da take yakin zaben 2015

- Wannan ya biyo bayan mayar da martani da yayi kan masu cewa Buhari na yin jinkiri wajen kaddamar da tsare tsare, inda ya ce hakan karya ce tsagwaronta

- Ministan, ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin APC ta kasance tana tafiya akan turbar da aka samar da ita, musamman wajen farfado da tattalin arzikin kasar

Ministan wuta, ayyuka da gidaje, Mr Babatunde Raji Fashola, a ranar Talata ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta APC bata taba cewa zata gyara kasar a cikin shekaru 4 ba, a lokacin da take yakin zaben 2015.

Wannan ya biyo bayan mayar da martani da yayi kan masu cewa shugaban kasa Buhari na yin jinkiri wajen kaddamar da tsare tsare, inda ya bayyana hakan a matsayin karya tsagwaronta, duba da irin ayyukan raya kasa da aka kaddamar a shekarun da ya dauka saman mulki.

Fashola ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da wata kungiyar yakin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari-Osinbajo 2019, da ta hada da sojin siyasa na kasa, da zasu karade dukkanin gundumomin da ke jihar Legas, don tabbatar da samun kuri'u akalla 4.5m da zasu tabbatar da nasarar tazarcen Buhari-Osinbajo a 2019.

KARANTA WANNAN: Goodluck Jonathan: Yadda Obama ya kitsa tuggun da ya zama silar faduwata zaben 2015

Dama can APC bata yiwa 'yan Nigeria alkawarin gyara kasar a cikin shekaru 4 ba - Fashola
Dama can APC bata yiwa 'yan Nigeria alkawarin gyara kasar a cikin shekaru 4 ba - Fashola
Asali: UGC

Ministan, ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin APC ta kasance tana tafiya akan turbar da aka samar da ita, musamman wajen farfado da tattalin arzikin kasar duk da irin yadda gwamnatocin baya suka lalata hanyoyin fardado da tattalin da kuma kwashe dukiyar kasar.

A cewar ministan, gwamnatin Buhari ta shimfida harsashe mai inganci na bunkasar tattalin arzikin Nigeria, da kuma yadda za a alkintasu, wanda a cewarsa, ya kamata 'yan Nigeria su kara sanya kyakkyawan yakini a shekaru masu zuwa, musamman duba da irin yadda gwamnatin yanzu ta gina kasar.

KARANTA WANNAN: Da zafi zafi: Buhari ya ki halartar taron kaddamar da littafin Jonathan a Abuja

"Bamu yi alkawarin canja Nigeria a cikin shekaru 4 ba. Mun yi iyakar bakin kokarinmu a kowanne fani, da ya hada da Ilimi. Misali a shekarar 2015, an kammala tituna masu tsawon kilo mita 80 ne kawai a fadin kasar. A 2016, an kammala ginin tituna masu tsawon kilimita 277. A 2017 kuwa, an gina tituna masu tsawon kilomita 488, yanzu kuma a 2018, an gina kilomita 497," a cewar Fashola.

A bangaren wuta kuwa, Fashola wanda shne tsohon gwamnan jihar Legas, ya ce shekaru 16 da suka gabata, ana samun megawatts 4,000 ne kawai na wutar lantarki, amma a cikin shekaru 3, an samar da wutar har zuwa megawatts 7,000.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng