Ba lallai bane Sule Lamido ya marawa Atiku baya a zaben 2019 - Hadimi

Ba lallai bane Sule Lamido ya marawa Atiku baya a zaben 2019 - Hadimi

- Akwai alamun cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, na iya janye goyon bayan da yake yiwa dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a zaben kujerar shuganan kasa

- Umar Danjani, mai tallafawa Mr. Lamido na musamman, ya ce ubangidansa bai ji dadin yadda kwamitin gudanar da yakin zaben jam'iyyar PDP ya mayar da shi saniyar ware ba

- Mr Danjani, ya ce kwamitin yakin zaben dan takarar shugaban kasa na PDP bai shirya cin zaben 2019 ba, duba da cewa sun ware mutane kamar Sule Lamido

Akwai alamun ceea tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, na iya janye goyon bayan da yake yiwa dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a zaben kujerar shuganan kasa. Mr. Lamido, na daya daga cikin wadanda suka tsaya takarar kujerar shugaban kasa a PDP, sai dai sun sha kasa a zaben fitar da gwani da ya gudana makonnin da suka shude.

Da yawa daga cikin yan takarar, shun sha alwashin marawa Atiku baya don tunkude shugaban kasa mai ci, Muhammadu Buhari daga kujerarsa a zaben 2019.

Sai dai, Umar Danjani, mai tallafawa Mr. Lamido na musamman, ya ce ubangidansa bai ji dadin yadda kwamitin gudanar da yakin zaben jam'iyyar PDP ya mayar da shi saniyar ware ba, tun bayan kammala zaben fitar da gwanin.

KARANTA WANNAN: Somin tabi: Shugaba Buhari ya tika Atiku da kasa a wani zaben gwaji da aka gunar a kasar Ingila

Ba lallai bane Sule Lamido ya marawa Atiku baya a zaben 2019 - Hadimi
Ba lallai bane Sule Lamido ya marawa Atiku baya a zaben 2019 - Hadimi
Asali: Twitter

A ranar Alhamis, a wani taro na masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP da ya gudana a sakatariyar jam'iyyar na jihar da ke garin Dutse, Mr. Lamido ya yabawa wakilan jam'iyyar kan zaben, inda ya bayyana cewa zaben da suka yi ne har ya baiwa wasu yan takara samun nasara.

"Dukkanin wanda kuka zaba, walau a matakin jihar ko kasa, shine yau yake da nasara, kuma kunyi ne don kashin kanku, sai dai gaskiya guda daya, shi sonkai kullum ke kai mutum ga da-na-sani," a cewar sa.

Wata majiya da ke da kusanci da Mr Lamido, ta shaidawa jaridar Premium Times cewa, Mr Atiku bai yiwa Mr Lamido adalci ba, kasancewar Lamido na daya daga cikin wadanda suka reni jam'iyyar PDP, kuma bai taba canja akala ba, sai dai an mayar da Lamido saniyar ware a harkokin jam'iyyar tun bayan da Atiku ya samu nasara a zaben fidda gwani.

Majiyar ta ce: "Abun da mamaki matuka, yadda suka gudanar da taro a Dubai da Abuja amma babu wamda aka gayyaci Lamido ko aka yi masa bayani kan abubuwan da suka faru. To wata kila dai ko taron na iyalan wadanda suka sauya sheka zuwa jam'iyyar ne don naga shuganam majalisar dattijai da kuma Kwankwaso a taron."

Haka zalika, Mr Danjani, ya shaidawa Premium Times cewa, kwamitin yakin zaben dan takarar shugaban kasa na PDP bai shirya cin zaben 2019 ba, "duba da cewa sun ware mutane kamar Sule Lamido, to tabbas Atiku ya manta kawai da samun nasarar zama shugaban kasa."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel