Kwankwaso tamkar gunki ne a gidan Makama - Ado Doguwa
Bulaliyar majalisar wakilan tarayya, Alhassan Ado Doguwa, ya yi kaca-kaca da tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata mai wakilar Kano ta tsakiya, Rabiu Musa Kwankwaso, a wani hira da ya gabatar da gidan talabijin TVC.
Hanarabul Ado Doguwa ya bayyana cewa Kwankwaso da kungiyarsa ta Kwankwasiyya ta zama tarihi a jihar Kano. Ya siffanta Sanatan a matsayin gunkin tarihi a gidan Makama.
Yace: "Kwankwaso da Kwankwasiyya tamkar gumaka ne a gidan Makama. Ko jar hulan da ake sanyawa ta zama tarihi a jihar Kano. Mutumin da ya sami kuri'u 158 kacal a zaben fidda gwanin PDP a Fatakwal, ko kashi 40 na delegets din jihar Kano basu zabeshi ba."
Ado Doguwa ya kara da cewa yan majalisan APC ba zasu tsige kakakin majalisa, Yakubu Dogara, ba muddin bai nuna bangaranci cikin majalisa ba kuma bai nuna adawarsa a fili ga shugaba Muhammadu Buhari.
A karshe, ya jaddada goyon bayansa ga jam'iyyar APC da shugaban jam'iyyar ta kasa, Adams Oshiomole. Kana ya bayyana cewa shugaba Buhari zai lashe zabe a jihar Kano.
Yace: "Za muyi duk abinda ke iya yiwuwa shugaba Muhammadu Buhari ya lashe zabe a jihar Kano."
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng