Rashi bisa rashi: Kwamishinonin Sule Lamido 2 sun sake juya masa baya
Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar a ranar Talata ya ƙara karɓar wasu kwamishinoni guda biyu da suka yi aiki da tsohuwar gwamnatin Sule Lamido ya zuwa jam'iyyar APC a gidan gwamnatin jihar Jigawa, garin Dutse.
Sabbin masu canza shekar sun haɗa da tsohon Kwamishinan Ayyuka na musamman Auwalu Harbo da tsohon Kwamishinan Noma Nasidi Ali, wanda ɗan takarar Sanatan Jigawa ta Arewa maso Yamma Sanata Danladi Sankara ya jagoranci shigowar su APCn a gidan Gwamnatin Jihar Jigawa dake Dutse.

Asali: UGC
KU KARANTA: Wani farfesan lissafi ya musulunta bayan nazarin Al'qur'ani
Legit.ng Hausa ta samu cewa Gwamna Badaru ya yi musu maraba tare da gode musu bisa wannan hoɓɓasa da suka yi na dawowa APC, inda yace hakan zai ƙarawa Jam'iyyar nasara wajen zaɓen Gwamna da na Shugaban Ƙasa.
Wannan yana zuwa ne bayan sati biyu da karɓar tsohon Kwamishinan shari'a Barista Nasiru Ruba da wasu tsoffin jigogin jam'iyyar PDP.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng