Albishir ga 'yan Nigeria: Mutane miliyan daya za su ci gajiyar shirin N-Power - Osinbajo

Albishir ga 'yan Nigeria: Mutane miliyan daya za su ci gajiyar shirin N-Power - Osinbajo

- Farfesa Yemi Osinbajo ya ce shirin N-Power da gwamnatin Buhari ta bullo da shi, za a fadada shi don baiwa mutane miliyan daya damar cikin gajiyar shirin

- Ya ce zuwa wannan lokaci, an dauki mutane 500,000, muna sa ran daukar wasu mutane 200,000 a shirin na gaba, wanda zamu rufe da wasu mutane 300,000 idan har damar hakan ta samu

- Ya kara da cewa gwamnati a halin yanzu ba zata iya biyan sama da N30,000 ga masu cin gajiyar shirin ba, a lokaci daya kuma ace ta gyara matsalolin rashin aikin yi a kasar

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce shirin N-Power da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bullo da shi, za a fadada shi don baiwa mutane miliyan daya damar cikin gajiyar shirin.

Osinbajo ya bayyana hakan a ranar Talata, cikin wata sanarwa daga babban mai tallafa masa ta fuskar kafofin sadarwa da watsa labarai, a ofishin mataimakin shugaban kasa, Mr Laolu Akande a Abuja.

KARANTA WANNAN: Ta tabbata: An sace katunan zabe 2,045 a ofishin INEC na jihar Akwa Ibom

Akande ya ruwaito Osinbajo ya na cewa hakan a lokacin da ya ke amsa tambayoyi a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja. Mataimakin shugaban kasar, ya ce an kirkiro da shirin N-Power a kokarin gwamnatin tarayya na samar da ayyuka kai tsaye ga jama'ar kasar musamman ma matasa.

Albishir ga 'yan Nigeria: Mutane miliyan daya za su ci gajiyar shirin N-Power - Osinbajo
Albishir ga 'yan Nigeria: Mutane miliyan daya za su ci gajiyar shirin N-Power - Osinbajo
Asali: UGC

"Zuwa wannan lokaci, mun dauki mutane 500,000, muna sa ran daukar wasu mutane 200,000 a shirin na gaba, wanda zamu rufe da wasu mutane 300,000 idan har damar hakan ta samu. Gaba daya dai, muna sa ran daukar mutane Miliyan daya aiki; wanda shine shiri mafi girma a fadin nahiyar Afrika.

"Dalilin da ya sa muke yin hakan ba zai wuce yadda ake fuskantar matsaloli na rashin ayyukan yi a kasar ba, mun san ba zamu iya daukar kowa aiki ba, amma ko ba komai, gwamnati za ta samar da wasu ayyukanyi na kai tsaye ga 'yan kasa," a cewar Osinbajo.

Ya kara da cewa gwamnati a halin yanzu ba zata iya biyan sama da N30,000 ga masu cin gajiyar shirin ba, a lokaci daya kuma ace ta gyara matsalolin rashin aikin yi a kasar. Sai dai ya ce, gwamnatin tarayya za ta samar da hanyoyin samun aikin yi, musamman a masana'antu.

"Idan an lura, zuwa yanzu, muna kan bunkasa tituna da layin dogo, hakan zai bunkasa masana'antunmu. Sannan mun samar da kasuwanni 300, mun yi a Ariaria a Kudu maso Gabas, Sabon Gari a Kano, Surat a Legas, Isikan a Ondo, Gbagi a Oyo da kuma sa ran fadadawa don baiwa jama'armu damar yin aiki."

Dangane da bukatar kara cusa mata a cikin ayyukan yi, Osinbajo ya bayyana cewa daya daga cikin muradun gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari shine shayar da mata romon demokaradiyya ta hanyar kirkiro da shirye shiryen na musamman, kamar shirin bayar da rance na Government Enterprise and Empowerment Programme (GEEP).

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng