Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ta dage zamanta saboda rashin kyan abun magana
- Majalisar wakilai ta dage zamanta na yau saboda rashin kyan abun magana
- Yakubu Dogara ya bayyana cewa akwai bukatar dage zaman domin samun damar gyara lasifar
- An dage zaman zuwa ranar Laraba, 14 ga watan Nuwamba 2018
Majalisar wakilai ta dage zamanta kan wata matsala da lasifikan majalisar ya samu.
Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana cewa akwai bukatar dage zaman domin samun damar gyara lasifar.
An dage zaman zuwa ranar Laraba, 14 ga watan Nuwamba 2018.

Asali: Depositphotos
Ya kuma bayyana cewa idan har matsalar ya ci gaba zuwa ranar Laraba, majalisar zata dage ama har sai illa-ma-shaa’a.
A cewar Dogara an dasa lasifikun ne a 1999 sannan kuma cewa fanel din zai kai makonni uku kafin ya iso Najeriya daga Jamus.
KU KARANTA KUMA: Sanata Sani ya bayyana manyan kalubale ga zaben 2019, ya nemi a zuba a idanu da kyau
A zaman yau wanda ya kwashe sama da sa’a guda, an gano yan majalisa suna mikawa junansu lasifika guda domin ba su damar tofa albarkacin bakinsu a zauren.
Wannan shine karo na biyu a mako guda da majalisar zata dage zama kan rashin kyan abun Magana.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng