Buhari ya ce kudaden Nigeria da aka sace an boye su a Amurka da kasashen Turai

Buhari ya ce kudaden Nigeria da aka sace an boye su a Amurka da kasashen Turai

- Shugaban kasa Muhamadu Buhari ya zargi masu fada a ji da rufe idanuwansu a lokacin da ake sace kudaden kasar da ya kamata ace anyi amfani da su wajen bunkasa fannin ilimi

- Buhari ya ce kasafin kudin ilimi na kasar da a yanzu yake kashi 5 kacal, bai ko kama kafar kashi 26 da majalisar dinkin duniya ta bada shawari akai ba

- Shugaban kasar ya bayyana cewa kudaden kasar da aka sace su aka boye a wasu kasashen Turai, za su iya kawo gagarumin canji idan aka sanyasu a fannin ilimi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kudaden da aka sace daga Nigeria, an boye su ne a kasashen Turai, Amurka da kuma wasu kasashen duniyar. Buhari ya bayyana hakan a ranar Litinin, 12 ga watan Nuwamba, a wata ganawa da yayi da 'yan Nigeria mazauna kasar Faransa.

A cikin wata sanarwa daga mai bashi shawara na musamman kan harkokin kafofin sadarwa da watsa labarai, Femi Adesina, wacce aka rabawa manema labarai a Abuja, na cewa shugaban kasa Buhari ya zargi masu fada a ji a kasar da juya baya a lokacin da ake sace kudaden da aka ware don fannin ilimi.

Shugaban kasar ya bayyana cewa kasafin kudin ilimi a yanzu, wanda ya ke kashi 5, ya yi matukar kadan, idan aka kwatanta da kashi 26 da majalisar dinkin duniya ta bada shawara akai. Sai dai ya baiwa 'yan Nigeria tabbacin cewa gwamnatinsa na kokari wajen bunkasa fannin ilimi kamar yadda take kokarin bunkasa tituna da layin dogo.

KARANTA WANNAN: Mun cika alkawuran da muka daukarwa 'yan Nigeria a fannin wuta, ayyuka da gidaje - Fashola

Buhari tare da 'yan Nigeria mazauna kasar Faransa
Buhari tare da 'yan Nigeria mazauna kasar Faransa
Asali: Facebook

Shugaban kasar ya ce "Tabbas da za a samu gagarumin ci gaba a fannin ilimi da anyi amfani da kudaden da aka sace a fannin, sai dai abun takaicin shine, har yanzu wasu mutane na da makudan kudade da suka boye a kasashen Turai, Amurka da wasu kasashen duniya, da ya kamata ace an bunkasa fannin ilimi da su."

Shugaban kasar ya roki masu fada aji a kasar da ke cikin gida da kuma kasashen ketare da su taimaka wajen bunkasa fannin ilimin kasar ta hanyar goyon bayan manufofi da kudurorin gwamnati.

A wani labarin makamancin wannan; shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da wasu matakai da za a bi ma-damar ana so a sake fasalin kasar, yana mai cewa dole ne a fara yin karatun ta-nutsu kan lamarin kafin ma a fara yunkurin daukar matakan sake fasalin.

Buhari ya ya kuma ce, 'yan Nigeria mazauna kasashen waje, ba za su iya shiga cikin wadanda za su iya kada kuri'a a zabukan kasar ba a halin yanzu, sai dai gwamnati nakokarin ganin ta samar da hanyar yin hakan a nan gaba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng