Hukumar Kwastam ta cafke mutane hudu tare da kama motocin alfarma da kayyakin N240m

Hukumar Kwastam ta cafke mutane hudu tare da kama motocin alfarma da kayyakin N240m

- Hukumar hana fasa kwabri ta kasa (Kwastam) ta gargadi masu fasa kwabri da su kauracewa wannan haramtacciyar sana'ar

- Hukumar ta ce a cikin yan kwanakin nan, ta cafke mutane 4, yayin da ta kwace motocin alfarma da aka shigo da su ba bisa ka'ida ba, da kudinsuya kai sama da N240m

- Ganin yadda shekarar ta zo karshe, hukumar ta ce suna ci gaba da fuskantar karuwar masu fasa kwabri, musamman a shiyyar Kudu maso Kudu, da kuma Kudu maso Yamma

Hukumar hana fasa kwabri ta kasa (Kwastam) ta gargadi masu fasa kwabri da su kauracewa wannan haramtacciyar sana'ar, domin kuwa hukumar ta dukufa ainun don bin matakan dakile kayayyakin da aka haramtawa shigowa da su kasar, musamman yanzu da lokacin bukukuwan kirsimeti ke gabatowa.

Kwanturolan hukumar na lardi, a sashen rundunar FOU, Zone C, Kayode Olusemire, ya karanta 'Dokar dakile fasa kwabri' ga masu safarar kaya zuwa kasar ta barauniyar hanya, ya ce Hukumarba zata yi kasa a guiwa ba wajen dakile shigowa da kaya, musamman shinkafa da motoci ta barayin hanyoyi.

KARANTA WANNAN: Shehu Sani: An kirkiro Sure-P, N Power don cimma bukatun siyasa ba don cigaban talaka ba

Hukumar Kwastam ta cafke mutane hudu tare da kama motocin alfarma da kayyakin N240m
Hukumar Kwastam ta cafke mutane hudu tare da kama motocin alfarma da kayyakin N240m
Asali: Depositphotos

Olusemire, wanda ya yi magana ga manema labarai a ofishin hukumar da ke Benin, ya ce a cikin yan kwanakin nan, hukumar ta cafke mutane 4, yayin da ta kwace motocin alfarma da aka shigo da su ba bisa ka'ida ba, da kudinsuya kai sama da N240m.

Range Rover, motoci kirar Toyota, miyagun kwayoyi kamarsu tabar Wiwi, daruruwan buhunan shinkafa da kuma sauran kayayyakin abinci, hukumar ta ce ta kwace a cikin yan kwanakin.

Kwanturolan ya ce, "Ganin yadda shekarar ta zo karshe, muna ci gaba da fuskantar karuwar masu fasa kwabri, musamman a shiyyar Kudu maso Kudu, da kuma Kudu maso Yamma, kuma a shirye muke da su. Muna gargadarsu akan cewa wadannan shiyyoyin ba kanwar lasa bane a wajensu, duk dabararsu, zamu cafke su."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel