Wata zankadediyar budurwa ta labarta yadda ta tsero daga gidan 'yan yankan kai a Najeriya

Wata zankadediyar budurwa ta labarta yadda ta tsero daga gidan 'yan yankan kai a Najeriya

Yayin da kasar nan ke cigaba da fuskantar barazanar tsaro daga bangarori da dama kama daga 'yan fashi da makami, barayi manya da kanana da kuma masu garkuwa da mutane, matsafa da masu yankan kanu ma ba'a bar su a baya ba.

Wani labarin da ya dauki hankulan 'yan Najeriya a 'yan kwanakin nan shine na wata mata da ta zayyana yadda Allah ya tarfawa garin ta nono ta samu ta kubuta daga hannun 'yan yankan kai.

Wata zankadediyar budurwa ta labarta yadda ta tsero daga gidan 'yan yankan kai a Najeriya
Wata zankadediyar budurwa ta labarta yadda ta tsero daga gidan 'yan yankan kai a Najeriya
Asali: UGC

KU KARANTA: Daya daga cikin wadanda Buhari ya hana fita ya sulale ya tafi Jamus

Legit.ng ta samu cewa matar dai wadda bamu tabbatar da sunan ta ba, ta zayyana hakan ne a shafin rubuntun ta dandalin zumunta na Whatsapp wanda kuma yake ta yawo a sauran kafafen sadarwar zamanin.

Budurwar dai ta bayyana cewa ta fito ne zata je shago siyayya to ashe motar da ta shiga ta 'yan yankan kai ce wadanda suka tafi da ita har gidan su tare da sauran jama'a da dama.

Sai dai kamar yadda tace, Allah ya taimake ta inda ta samu ta tsere ta wata kofa da ta gani a bude yayin da mutanen da suka kamo su suke takadda akan wadanda za'a fara yankawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng