Abu daya ne zai sa mu dena zanga-zanga a Abuja - Mabiya Shi'a

Abu daya ne zai sa mu dena zanga-zanga a Abuja - Mabiya Shi'a

- Mabiya Shi'a a Najeriya sun bayyana cewa sakin El-Zakzaky da sauran 'yan kungiyar da ke hannun jami'an tsaro ne kawai zai sa su dena tattakin

- Wani shugban kungiyar, Abdullahi Muhammad ya ce harin da jami'an tsaro ke kai musu ba zai hana su cigaba ba

- Ya ce muddin jami'an tsaron ne da harsasai da za suyi asara, 'yan kungiyar suna da kirjin karbar hasasan

Abu daya ne zai sa mu dena zanga-zanga a Abuja - Mabiya Shi'a
Abu daya ne zai sa mu dena zanga-zanga a Abuja - Mabiya Shi'a
Asali: Facebook

A jiya, Talata ne 'yan Kungiyar Ismlamic Movement of Nigeria (IMN) suka bayyana cewa ba za su taba dena tattakin da su ka fara a Abuja ba har sai lokacin da gwamnati ta sako shugabansu Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da matarsa daga inda ake tsare su tun shekarar 2015.

Bayan artabun da su kayi da jami'an tsaro, daya daga cikin shugabanin kungiyar, Abdullahi Muhammad ya shaidawa manema labarai cewa ba za su dena tattakin ba duk da harin da jami'an tsaro ke kai musu.

DUBA WANNAN: Yadda muka kama 'yan Shi'a dauke da bama-bamai - 'Yan Sanda

Ya ce idan gwamnati na son su dena tattakin, su saki shugabansu da matarsa da sauran mambobin kungiyar da jami'an tsaro suka tsare.

A cewarsa, "ba za mu dena tattakin ba har sai lokacin da suka aikata abin da ya dace. Idan suna so su cigaba da kashe mambobin mu, idan suna da harsasai da za suyi asara, mu kuma muna da kirgin karabar harsashen."

Kazalika, wata kungiyar kirista, Young Christian Forun (YCF) reshen Abuja ta janyo hankalin mutane kan artabun da jami'an tsaro keyi da mabiya Shi'a a Abuja wanda ke janyo asarar dukiya da rayyuka a Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164