Ezekwesili: Hanyoyin da zanbi don samun nasara akan Buhari da Atiku a zaben 2019
- Dr. Oby Ezekwesili, ta bayyana hanyoyin da zata bi don samun nasarar kayar da shugaban kasa Buhari da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
- Ta ce zabar Atiku ko Buhari tamkar ka tambayi mutum ya zaba tsakanin mutuwa ta hanyar shan guba ko harbi da bindiga ne
- Tsohuwar ministar, ta jaddada cewa ita ce kadai yar takarar da ta fi dacewa yan Nigeria su zaba a matsayin shugabarsu a 2019
Tsohuwar ministar Ilimi, kuma yar takarar shugabar kasa karkashin jam'iyyar ACPN, Dr. Oby Ezekwesili, ta bayyana hanyoyin da zata bi a lokutan yakin zabenta, wadanda za su bata nasarar kayar da shugaban kasa mai ci Muhammadu Buhari da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Ezekwesili, wacce ta bayyana hakan a wani taron 'yan jaridu a Legas, ta kuma ce da Buhari da Atiku kamar mutum daya ne a wajenta ba wai 'yan takara biyu ba "saboda jam'iyyar APC da Buhari ke takara a ciki, da PDP da Atiku ke takara a ciki, kamar dan jumma da dan jummai ne, lallai faduwa na wajensu gaba daya."
Ta ce: "Babu wani mai dama dama a 'BuTiku; BuTiku' mambobin jam'iyya daya ne. Zabar daya daga cikin wadannan mutanen biyu kamar ka tambayi mutum ya zaba tsakanin mutuwa ta hanyar shan guba ko harbi da bindiga. Allah ya kiyaye. Mun gaji da wahalhalun da muke ciki, Allah ma ya gani kuma ba zaya bamu wanda zai hana mana rawar gaban hantsi ba."
KARANTA WANNAN: Gaskiyar dalilin da ya sa gwamnatin Buhari ta sanya aka kamani - Olisa Metuh

Asali: UGC
Ta kara da cewa: "Ina mamaki da yin dariya a duk lokutan da na ji jama'armu na cewa, wannan yunkuri namu zai kawo rabuwar kuri'u. Sai dai fa PDP ba abokiyar hamayyar APC ba ce. Dan takarar PDP a cikin shekaru 14 ya sauya sheka daga PDP zuwa AC, daga AC zuwa PDP, daga nan yankoma APC, yanzu kuma ya koma PDP. Don haka wadannan mutanen kamar kannai da yayye suke, kowannensu faduwa ce ke binsa,
"Kar ku kuskura ku yarda da wannan damfarar ta yan 419! Gaba dayansu sun fito ne daga jam'iyyun da suka mulke mu, mun ganyadda suka yaudaremu, suka wargazamu tsawon shekaru. Yanzu kuma suna so su sake maimaita asarar da suka jawo mana har na tsawon wasu shekaru 4? Allah ya kiyaye faruwar hakan!," cewar Ezekwesili.
Tsohuwar ministar, wacce ta zayyana ayyukan da ta gabatar, yadda ta dade tana son shiga harkokin siyasa da kuma kudirinta na shiga takarar kujerar shugaban kasa, ta jaddada cewa ita ce kadai yar takarar da ta fi dacewa yan Nigeria su zaba a matsayin shugabarsu a 2019.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng