Rigimar APC: An yi zanga-zanga a Neja saboda wasu sun rasa tikitin takara
Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa an yi ta faman zanga-zangar siyasa a Jihar Neja a game da sunayen ‘Yan takaran da Jam'iyyar APC mai mulki ta mikawa Hukumar zabe watau INEC na zaben 2019.

Asali: Depositphotos
Magoya bayan Jam’iyyar APC mai mulki sun yi zanga-zanga a cikin Jihar Neja inda wasu ‘Yan Majalisu su ka koka da sakamakon zaben fitar da gwani da aka yi su na masu neman zuwa har gaban Kotu domin a fitar masu da hakkin su.
Wasu ‘Yan takaran sun bayyana cewa su ne su ka lashe zaben fitar da gwani amma sai aka cire sunayen su daga cikin wadanda su ka samu tutan takara aka kakaba na Abokan adawar ta su. Wannan dai ya jawo rikici ainun a Jam’iyyar.
KU KARANTA: Shugaba Buhari yana kokarin dinke barakar da ta shigo APC kafin 2019
Daya daga cikin masu neman kujerar Majalisar Tarayya a mazabar Rijau, Jafaru Ilyasu bayyana cewa an cire sunan sa an sa wani Hon. Shehu Saleh Rijau wanda bai ma yi takara ba don haka yace zai sheka Kotu domin gaskiya tayi halin ta
Shehu Rijau bai saye fam din takarar Majalisa ba inji Abokin adawar ta sa kurum sai aka ji cewa shi ne zai yi takara a 2019. Wani ‘Dan takaran Yankin Suleja ya nuna cewa shi ma zai maka APC a gaban Kotu saboda irin wannan dalili.
Mun samu labari wadanda su ka yi takara su ka fadi za su garzaya Kotu su kai karan Jam’iyyar APC a Jihar Neja. Daga cikin akwai wani mai neman Majalisa a mazabar Rijau mai suna Jafaru Ilyasu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng