Namu ya samu: Dangote ya samu babbar karramawa a tsakankanin masu kudin duniya

Namu ya samu: Dangote ya samu babbar karramawa a tsakankanin masu kudin duniya

- Dangote ya samu babbar karramawa a tsakankanin masu kudin duniya

- Dangote ya zama na 6 a duniyar masu taimakon al'umma

- Dangote dan Arewa ne daga jihar Kano

Fitaccen attajirin nan, wanda yafi kowa kudi a Nahiyar Afrika, kuma daya daga cikin masu kudin duniya watau Alhaji Aliko Dangote da ya fito daga jihar Kano dake a Arewacin Najeriya ya samu karramawa babba daga wata Mujalla a kasar Ingila.

Namu ya samu: Dangote ya samu babbar karramawa a tsakankanin masu kudin duniya
Namu ya samu: Dangote ya samu babbar karramawa a tsakankanin masu kudin duniya
Asali: UGC

KU KARANTA: Yan Boko Haram sun kashe wani basarake a Arewa

Mujallar mai suna Richtopia dake buga labaran ta akan bangarorin kudi da tattalin arziki musamman ma wadanda suka shafi Nahiyar Afrika, ta kuma yiwa wasu shahararrun masu kudin duniyar irin wannan karramawar.

Legit.ng Hausa ta samu cewa Warren Buffett, Bill Gates da kuma J.K Rowlings sune suka samu matsayi na daya, biyu da kuma ukku yayin da kuma Oprah Winfrey da kuma Elon Musk suka samu matsayi na hudu da da na biyar.

Haka ma dai shugaban bankin UBA, Mista Tony Elumelu shi ma ya samu wannan karramawar a matsayi na sha daya a duniya, kuma na biyu a Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng