Ba zamu kakaba tsarin kayyade haihuwa ba, burinmu bada tazarar haihuwa - Zainab Ahmed
A ranar Larabar nan, Ministar kudi, Zainab Ahmed, ta karyata rahotannin da ke yawo na cewar gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari, zata kakaba tsarin kayyade adadin 'yayan da maya zasu haifa a kasar.
Kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter, @ZShamsuna, Ahmed ta ce, gwamnati na kokarin karfafa guiwar shuwagabannin addinai dana gargajiya don fadakar da jama'arsu dangane da muhimmancin bada tazarar haihuwa.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Buhari za ta kayyade adadin 'yayan da kowacce uwa zata haifa

Asali: Depositphotos
Jawabin nata kamar yadda ta wallafa na cewa: "Gwamnatin tarayya ta dade tana tuntubar masu ruwa da tsaki, kamar shuwagabannin gargajiya dana addinai wajen fadakar da jama'a dangane da muhimmancin bada tazarar haihuwa.
"Bamu taba cewa zamu kakaba tazarar haihuwar dole ko kayyade yawan 'yayan da mata zasu haifa ba. Shin me ake ma nufi da bada tazarar haihuwa? Wannan wani lokaci ne na bada hutu tsakanin haihuwa da daukar wani cikin, kuma yana da matukar amfani ga lafiyar iyaye mata."
A ranar Talata ne ministar kudin, a wani taron tattalin arzikin Nigeria karo na 24 da ya gudana a Abuja, ta ce gwamnati na kokarin bullo da wani sabon tsari da zai kayyade adadin 'yayan da kowacce uwa zata haifa a kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Asali: Legit.ng