Barayin da suka yi garkuwa da basarake a Kaduna sun saki matarsa

Barayin da suka yi garkuwa da basarake a Kaduna sun saki matarsa

Masu garkuwan da suka sace matar Shugaban Adara a karamar hukumar Kachia, jihar Kaduna, Misis Victoria Galadima sun sake ta a safiyar ranar Lahadi, 21 ga watan Oktoba.

Da yake tabbatar da sakin nasa, kakakin rundunar yan sandan Kaduna, DSP Yakubu Sabo yace a yanzu haka matar na ganin likita a babban asibitin Kachia.

A cewar sa ana nan ana kokari don tabbatar das akin mijin nata, Dr Maiwada Galadima, wanda ke a hannun masu garkuwa da mutanen har yanzu tare da direbansa wanda aka kira da suna Timothy.

Barayin da suka yi garkuwa da basarake a Kaduna sun saki matarsa
Barayin da suka yi garkuwa da basarake a Kaduna sun saki matarsa
Asali: Depositphotos

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa mutane hudu harda jami’in dan sanda masu karkuwa da mutanen suka kashe a ranar Juma’a, kafin su tafi da basaraken, matarsa da direbansu.

KU KARANTA KUMA: An kwantar da masoyin Atiku da yayi tattaki daga Owerri zuwa Abuja akan keke a gadon asibiti

A wani lamari na daban, mun ji cewa ‘yan ta'addan Boko Haram sun shiga Kauyukan da ke cikin Garin Konduga a jiya da dare inda su ke cigaba da ta’adi kamar yadda mu ka samu labari daga Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN.

Ba a wuce awa 12 da harin da Boko Haram su ka kai a Yankin Molai da ke cikin Karamar Hukumar Jere ba sai aka ji cewa an sake kai wani danyen hari a Garuruwan Mairari da Femari da ke cikin Jihar Borno inda su kona gidaje.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng