Kwadago: Zamu zabi shugaba ne kawai a 2019, wada zai kawo cigaban masana'antu
- Zamu zabi jagora ne wanda zai kawo cigaba a harkar masana'antu
- Ya zama dole Nageriya ta dunga sarrafa mana kayan sawa,samar mana da ayyukan yi
- Ya kamata kasar ta samar da hanyoyin da za'a samar da wutar lantarki

Asali: Depositphotos
Mambobin kungiyar da ke samar da kayan sawa da kuma madinka ta Nageriya NUTGTWN tace zasu zabi Shugaba wanda zai kawo cigaba a harkar kasuwanci a zaben 2019.
Sun bayyana hakan ne a wani kira da sukayiwa gwamnatin tarayya akan sarrafa kayayyaki a kasar nan.
Da yake tofa albarkacin bakin sa Mr Issa Aremu yace "a zaben 2019 da za'a gudanar ya'yan kungiyar mu zasu zabi tankarar da zai kawo cigaba a bangaren kasuwan ci da kuma masana'antu".
"bamu damu ba idan yazo a na farko,na biyu,na uku,ko na hudu,mudai fatan mu ya zama dole Nageriya ta dunga samar mana da kayan sawa,samar mana da ayyukanyi sannan dole Najeriya ta dakatar da fitar da auduga, danyen mai da kuma albarkatun kasa zuwa China, Europe da kuma Japan."
DUBA WANNAN: An kamo masu kokarin kashe shugaban kasa
A bangaren wuta kuma yayi kira ka gwamnatin da tayi kokari wajen samar da tsayayyiyar wutar lantarki,duba da cewa karancin wutar yana durkusar da masana'an tu.
A bangaren sa Alhaji Hassan Sumonu yace abu ne mai matukar wahala ga Nageriya ta dunga samar da kayayyakin amfanin yau da kullum da kanta matukar bata gyara sha'anin wutar lantarki ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng