Karon farko bayan bullar bidiyon rashawa, Buhari ya hadu da Gwamna Ganduje
- Karon farko bayan bullar bidiyon rashawa, Buhari ya hadu da Gwamna Ganduje
- Ganduje ya jagoranci 'yan Tijjaniya zuwa wurin Buhari
- Buhari ya godewa 'yan Tijjaniyya
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya hadu da gwamnan Kano, Dakta Abudllahi Umar Ganduje karon farko tun bayan bullar faifan bidiyon nan da aka fallasa na sa yana karbar cin hanci na miliyoyin daloli a satin da ya shude.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Buhari ya yabawa Obasanjo kan namijin kokarin sa
Shi dai gwamnan na Kano, mun samu labarin yayi wa shugabannin majalisar zartarwa na darikar Tijjaniyya ne jagora zuwa ga shugaban kasar a fadar sa dake a birnin tarayya Abuja ranar Juma'ar da ta gabata.
Legit.ng Hausa ta samu cewa a yayin tattaunawar wadda suka yi, shugaban kasar ya yabawa 'yan darikar na Tijjaniya bisa irin gudmmuwar da suke baiwa kasar wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya tare da rokon su da su cigaba.
Su ma da suke mayar da jawabi, Ibrahim Maihula dake zaman jagoran su a ziyarar ya tabbatar wa shugaban kasar da dukkan cikakken goyon bayan su ga kyawawan manufofin shugaban kasar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng