Gwamnatin tarayya ta haramtawa Radio Nigeria tattaunawar kai tsaye da Omoyele Sowore

Gwamnatin tarayya ta haramtawa Radio Nigeria tattaunawar kai tsaye da Omoyele Sowore

- Omoyele Sowore ya yi ikirarin cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayar da umurni, na dakatar da Radio Nigeria daganyin hira da shi

- Ya bayyana takaicinsa kan wannan hukunci da gwamnatin tarayyar dama gidan Radio Nigeria suka yanke na dakatar da wannan hira

- Ya yi zargin cewa anyi hakan ne don dakile shi daga fallasa wasu laifuka na gwamnatin shugaban kasar Buhari

A ranar Alhamis ne gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta baiwa hukumar da ke kula da gidajen Rediyo ta kasa (FRCN), umurnin soke hirar da gidan Rediyon ta shirya gudanarwa da dan takarar jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, akan abun da wasu ke kira tsoron tonon silili.

Gidan Radio Nigeria, da ke Abuja, ya shirya gudanar da wata hira ta awa daya da Sowore, wacce zata zama kai tsaye ga masu sauraro a fadin kasar, sai dai 'yan mintoci kadan da wannan yarjejeniyar, gidan Rediyon ya fitar da sanarwar cewa an soke wannan yarjejeniya 'daga sama'.

Dan takarar jam'iyyar ta AAC, ya bayyana takaicinsa kan wannan hukunci da gwamnatin tarayyar dama gidan Radio Nigeria suka yanke na dakatar da wannan hira da aka shirya yi da shi.

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: Hukumar NHIS ta dakatar da babban sakatarenta har sai baba-ta-gani

Gwamnatin tarayya ta haramtawa Radio Nigeria tattaunawar kai tsaye da Omoyele Sowore
Gwamnatin tarayya ta haramtawa Radio Nigeria tattaunawar kai tsaye da Omoyele Sowore
Asali: Depositphotos

Kamar yadda yake cewa a shafinsa na sada zumunta na Twitter:

"Wasu jiga jigai a FRCN, sun soke hirar da gidan rediyon ya shirya gudanarwa da ni da misalin karfe 4 na yammacin yau a babbar tasharsu da ke Abuja, bayan da suka gano cewa da nine za ayi hirar, don haka aka bayar da umurnin dakatar da hirar 'daga sama'."

Masu fashin baki kan harkokin siyasa, na kallon wannan mataki da aka dauka kan Sowore, a matsayin hanyar dakile shi daga fallasa wasu laifuka na gwamnati, ko kuma amayar da wasu boyayyun al'amura da ka iya zama turnuku a siyasar jiga jigan kasar da dama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng