Saraki ya ga uwar bari, ya biya Omo-Agege hakkinsa
Rahotanni sun kawo cewa biya Sanata mai wakiltan Delta ta tsakiya, Ovie Omo-Agege dukka hakkinsa bayan majalisar ta dakatar da shi ba bisa ka’ida ba a farkon shekarar nan.
Ci gaban wanda ke zuwa a ranar Alhamis, 18 ga watan Oktoba ya kawo karshen karar da Omo-Agege ya shigar a gaban babbar kotun tarayya kan shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.
Lauyan Omo-Agege, Dr. Alex Izinyon (SAN), ya sanar da Justis Nnamdi Dimgba a ranar Alhamis cewa an biya wanda yake karewa hakkinsa a ranar 12 ga watan Oktoba, kasa da sa’o’i 24 bayan kotu ta gargadi Saraki akan ya biya bashin ko kuma ya gurfana a gaban kotu.

Asali: Depositphotos
Justis Dimgba yayi gargadin ne a ranar 11 ga watan Oktoba bayan ya sake ba Sarak damar da zai gyara laifinsa akan zargin da ake masa.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An tabbatar da Bindo a matsayin dankarar gwamna na APC a Adamawa
Babban lauyan yace an gabatarwa da sanatan takardan kudi na banki a ranar 12 ga watan Oktoba kuma ya sanya hannu.
Ya kuma bayyana cewa a lokacin da aka gabatar masa da takardan ya lura akwai sauran naira milyan shida inda hadimin shugaban majalisar ya amince da hakan cewa kuskure aka samu wajen na’urar.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa an ba sabbin sanatoci daga jihohin Katsina da Bauchi, Ahmed Babba Kaita da Lawal Yahaya Gumau mukaman shugabantar wasu kwamiti daban-daban.
Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, wanda ya sanar hakan a jiya Laraba, 17 ga watan Oktoba a zangon majalisa, yace Kaita ya zama shugaban kwamitin kasuwanci, yayinda Gumau zai jagoranci shugaban kwamitin kawar da talauci.
Asali: Legit.ng