Bamu aike ka yin satar jarabawar WAEC ba, ka je ka kare kanka - APC ta caccaki Adeleke

Bamu aike ka yin satar jarabawar WAEC ba, ka je ka kare kanka - APC ta caccaki Adeleke

- APC ta bukaci Sanata Ademola Adeleke, da ya fuskanci tuhumar da ake masa na satar jarabawar WAEC

- APC ta yi shagube da cewa ba jam’iyyar bace ta aike shi ya je yayi satar amsa a tun farko

- Adeleke dai ya zargi jam’iyyar APC da rundunar yan sanda na hada baki wajen hana shi kai kara kotu, don korafi kan zaben gwamnan jihar Osun da ya gudanar

Jam’iyyar APC ta bukaci dan takarar PDP a zaben gwamnan jihar Osun da ya gabata, Sanata Ademola Adeleke, da ya fuskanci tuhumar da ake masa na satar jarabawar WAEC, kana ya cire jam’iyyar APC daga wannan tuhumar don ba it ace ta turashi yin satar amsar ba.

APC ta ce Adeleke ya kuka da kansa, kasancewar shine ya cusa kansa a cikin harkallar satar jarabawar, tana mai cewa jam’iyyar ba ta ce ya je yayi satar amsa a tun farko ba. Rundunar ‘yan sanda ne dai ke zargin Adeleke da satar amsar jarabawar WAEC.

Daraktan watsa labarai, bincike da tsare tsare na jam’iyyar APC a jihar Osun, Mr. Kunle Oyatomi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Osogbo a ranar Laraba, a matsayin martani kan zargin da Adeleke ya ke yiwa jam’iyyar ta APC.

KARANTA WANNAN: Yan Nigeria miliyan 93 ne ke rayuwa ba tare da hasken wutar lantarki ba - Cibiyar kasashen waje

Bamu tura ka yin satar jarabawar WAEC ba, ka je ka kare kanka - APC ta caccaki Adeleke
Bamu tura ka yin satar jarabawar WAEC ba, ka je ka kare kanka - APC ta caccaki Adeleke
Asali: Depositphotos

Sanarwar ta ce “Wannan matsalar tsakanin Adeleke da rundunar ‘yan sanda ne. Kuma mu ba yan sanda masu shigar da kara bane. Idan har yan sanda ne suka kaishi kotu, to ina ruwan APC a ciki?

“Shine ai yakai maganar gaban kotu, don haka ya rage nasa ya je ya kare kansa a gaban kotun. Mu ba zamu iya hana kotu ta gudanar da aikinta ba, hatta shi kansa Ademola bai isa ya hana kotu gudanar da ayyukanta ba.

“Don haka zai zama yarinta da rashin dogon Tunani har Ademola ya zargi APC da rundunar yan sanda na hadin baki wajen hana shi gabatar da korafinsa, ko kuma dai wata kila Adeleke ya shantake wajen rawar banjo mai makon mayar da hankali kan sanin yadda kotun zata gudanar da hukuncinta.”

Adeleke dai ya zargi jam’iyyar APC da rundunar yan sanda na hada baki wajen hana shi kai kara kotu, don korafi kan zaben gwamnan jihar Osun da ya gudanar, yana mai zargin sun bijiro da batun satar amsar jarabawa ne don dakile shi shigar da kara kan zaben.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng