Hukumar Kwastam ta cafke kayayyakin Abinci da kudinsu ya kai N30m a Kano

Hukumar Kwastam ta cafke kayayyakin Abinci da kudinsu ya kai N30m a Kano

- Hukumar Kwastam, reshen Kano/Jigawa, ta samu nasarar cafke kayayyakin abinci da kudinsu ya kai sama da N30m a jihar Kano

- Kayayyakin da hukumar ta cafke sun hada da Shinkafa yar kasar waje, Man dafa abinci, Sukari da kuma taliyar Spaghetti

- Hukumar ta ce ba zata gajiya a kokarinta na hana fasa kwabrin kayayyakin da aka haramta shigowa da su kasar ba

Hukumar hana fasa kwabri ta kasa (Kwastam), reshen Kano/Jigawa, ta samu nasarar cafke kayayyakin abinci da kudinsu ya kai sama da N30m a jihar Kano, kamar yadda kwanturolan hukumar na jihar, Nasir Ahmad ya bayyana.

Da yake jawabi ga manema labarai a jiya Talata, 17 ga watan Oktoba a Kano, Ahmad ya ce kayayyakin abincin sun hada da buhuna 1,200 na shinkafa yar kasar waje da kudinta ya kai N26,863,200, jarkoki 300 na man dafa abinci da kudinsu ya kai N3,476,340, buhuna 100 na sukari dan kasar waje da kudinsu ya kai N2,178,500 da kuma katon 200 na taliyar Spaghetti yar kasar waje, da kudinta ya kai N402,620.

KARANTA WANNAN: Yan Nigeria miliyan 93 ne ke rayuwa ba tare da hasken wutar lantarki ba - Cibiyar kasashen waje

Hukumar Kwastam ta cafke kayayyakin Abinci da kudinsu ya kai N30m a Kano
Hukumar Kwastam ta cafke kayayyakin Abinci da kudinsu ya kai N30m a Kano
Asali: Depositphotos

Ahmad ya ce anyo safarar kayayyakin ne ta cikin garuruwan Daura, Gwarzo, Bichi da kuma Babura, yana mai nuni da cewa an yi amfani da motoci 14 wajen fasa kwabrin kayayyakin zuwa cikin kasar har zuwa jihar Kano.

Kwanturolan ya ce hukumar ta cafke mutane 5 da ake zargin su da sanya hannu a shigowa da kayan, yana mai bada tabbacin cewa za su gurfanar da su da zaran hukumar ta kamala gudanar da bincike.

Ya ce: “Ba zamu gajiya a kokarinmu na hana fasa kwabrin kayayyakin da aka haramta shigowa da su kasar ba. Wadannan mutane, su ke durkusar da tattalin arzikin kasar, mu kuma ba zamu tsaya muna kallonsu don kai kasar ga halin ni-‘yasu ba."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details…

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng