Bakin alkami ya bushe: APC ba ta da 'yan takara a zaben 2019 na jihar Zamfara - INEC
- Hukumar INEC, ta kara jaddada matsayarta, na cewar jam'iyyar APC bata da 'yan takara a babban zabe na 2019 a jihar Zamfara
- Farfesa Yakub ya ce tuni dama hukumar ta bayar da sanarwar wannan matakin nasu a Zamfara, kuma ba zasu sauya akalar matakin ba
- Sai dai Adams Oshiomhole, ya ce tuni jam'iyyar APC ta zabi yan takararta na jihar Zamfara tun kafin wa'adin hukumar ya kare
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta kara jaddada matsayarta a jiya, na cewar jam'iyyar APC bata da 'yan takara a babban zabe na 2019 a jihar Zamfara.
Shugaban hujumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya jaddada hakan a wani taron bita na kwana 2 da aka shirya kan nazarin kudaden da ake kashewa wajen gudanar da zabe a yankunan kasashen Afrika ta Yamma.
Farfesa Yakub ya ce tuni dama hukumar ta bayar da sanarwar wannan matakin nasu a Zamfara, kuma ba zasu sauya akalar matakin ba, yana mai cewa "zamu ci gaba da martaba wannan sanarwa da muka bayar ba tare da mun sauka daga kanta ba."
Yakub ya tariyo cewa hukumar ta bayar da wa'adin karbar sunayen yan takara daga jam'iyyu, wanda ya kare a ranar 18 ga watan Oktoba, yana mai cewa hukumar zata fitar da cikakken rahoto kan hakan a ranar 18 ga watan Nuwamba.
KARANTA WANNAN: Mun yi iya bakin kokarinmu na ganin ta kubuta - Matsayar gwamnatin tarayya kan kisan Hauwa Leman

Asali: Depositphotos
A baya bayan nan ne dai INEC ta aikawa jam'iyyar APC wata budaddiyar wasika, tana mai sanar da ita cewa ba zata bata damar sanya yan takararta a babban zaben jihar Zamafara na 2019 ba.
Sakataren hukumar na kasa, Okechkwe Ndeche, a wasikar da yanaikawa APC, ya ce hukumar ta haramtawa APC yin takarar kujerar gwamna, yan majalisun tarayya dana dokoki, sakamakon karya dokar da APC ta yi na hukumar, a sashe na 87 da 31 na dokar zabe ta kasa.
Sai dai shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya mayarwa hukumar INEC da martani a cikin wata sanarwa, inda ya ce tuni jam'iyyar ta zabi yan takararta na jihar Zamfara tun kafin wa'adin hukumar ya kare.
Oshiomhole ya ce kasancewarba sai an gudanar da zabe ne kadai jam'iyya ke iya fitar da yan takara ba, "to kuwa muna tsaye kyam akan bakarmu na cewar tuni mun fitar da yan takararmu ta hanyar wakilci a otel din City King da ke garin Gusau, jihar Zamfara."
Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng