Shu’uma: Na samu damar kashe maza har 4 ta hanyar yin basaja da hijabi – Wata budurwa

Shu’uma: Na samu damar kashe maza har 4 ta hanyar yin basaja da hijabi – Wata budurwa

Mariam Abiola, wata shaidaniyar budrwa mai shekaru 20 ‘yan kungiyar asiri ta “Eiye” ta bayyana yadda ta kashe wasu mutane har 4 daban-daban a yankin Ilasamaja ta jihar Legas ta hanyar yin basaja das aka hijabi.

Mariam, da jami’an ‘yan sanda na ofishin Ilasamaja suka kama da safiyar yau, Litinin, ta bayyana cewar ta daina zuwa makaranta ne tun tana aji uku na makarantar sakandire.

An kama ta ne tare da wasu karti 4 a wani sintiri da jami’an ‘yan sanda karkashin shugabansu na ofishin yankin Ilasamaja ya jagoranta.

Shu’uma: Na samu damar kashe maza har 4 ta hanyar yin basaja da hijabi – Wata budurwa
Mariam, budurwa mai shekaru 20

Da take yiwa jami’an ‘yan sanda bayanin hanyar da take bi kafin kasha ‘yan kungiyar asiri dake hamayya da tasu, Mariam ta bayyana cewar tan a samun saukin gudanar da aiyukanta na ta’addanci ta hanyar saka hijabi bayan shugabannin kungiyarta sun tsuma tad a asiri.

Matashiyar ta bayyanawa ‘yan sanda cewar ta zo Legas ne daga jihar Osun domin neman aiki amma sai wani saurayi, Saddiq, day a sauketa ya saka ta cikin kungiyar su ta asiri.

DUBA WANNAN: Batanci: Jami'an tsaro sun mamaye makarantar da wani dalibi ya zagi annabi

Kazalika ta bayyana cewar saddiq din ne ke biyanta N10,000 duk lokacin da ta kasha wani mutum.

Saidai Saddiq ya musanta sanin matashiyar duk da ya amince cewar shi dan kungiyar asiri ta “Eiye” ne.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Edgal Imohimi, ya nuna matukar kaduwa da jin maganganun dake fitowa daga bakin Mariam tare da yin kira ga iyaye das u saka ido a kan irin abokai ko kawaye da ‘ya’yansu ke wasa ko yawo tare.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng