Bayan ta gaji faduwa zabe, PDP ta kafa kwamitin canja suna da inkiya

Bayan ta gaji faduwa zabe, PDP ta kafa kwamitin canja suna da inkiya

- Rahotanni sun bayyana cewar jam'iyyar hamayya ta PDP ta fara yunkurin canja sunanta kafin zaben 2019

- Ta nada mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Ike Ekweremadu, ya jagoranci kwamitin nemo sabon sunan da zata canja

- Jam'iyyar na son canja sunan ne domin kara samun damar lashe kujeru a zaben 2019

Wani sabon rahoto dake zuwa daga sansanin jam'iyyar adawa ta PDP na nuni da cewar ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattijai Sanata Ike Ekweremadu domin nemo mata sabon suna.

Bayan ta gaji faduwa zabe, PDP ta kafa kwamitin canja suna da inkiya
Ike Ekweremadu

Jaridar Thisday ta rawaito cewar, PDP na son canja sunanta ne biyo bayan asarar kujeru da take yi a zabukan da ake yi a fadin kasar nan.

Rahoton ya kara bayyana cewar, PDP zata canja suna ne domin gujewa yawaitar alakanta sunanta da cin hanci da jam'iyyar APC mai mulki ke yi.

DUBA WANNAN: Fadan karshe: R-APC ta gabatarwa da Buhari da APC bukatu 7 kafin ganawar karshe da zasu yi yau

Jaridar ta wallafa cewar a yau, Lahadi, ne PDP zata sanar da wannan shawara da ta yanke ga jama'a tare da kaddamar da kwamitin nemo mata sabon suna da inkiya da Ekweremadu zai jagoranta.

Canjin sunan na daga cikin dalilan da wasu 'yan APC, musamman tsagin R-APC, ke bukatar a yi kafin su shigo jam'iyyar ta PDP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng