Kalli takardun kammala karatun minista Kemi da shaidar NYSC din ta na karya
Rahotanni sun kawo cewa takardar shaidar bautar kasa da ministar kudi, Kemi Adeosun ta mallaka na jabu ne.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa hakan na zuwa ne shekaru da yawa bayan ta kammala jami’a.
Dokar Najeriya ta tanaji hukunci ga mutumin da duk ya ki zuwa aikin bautar kasa da gangan matsawar dai bai cika shekaru 30 ba.
Takardun karatun Kemi da jaridar Premium Times ta wallafa sun nuna cewa hukumar ta ba ta takardun shaidar yafe mata zuwa bautar kasa a shekarar 2009, a bisa yawan shekaru.
Ga hotunan a kasa:
KU KARANTA KUMA: Muna da hujja akan yan siyasar dake da hannu a kashe-kashe – Fadar shugaban kasa
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng