Tafiyar hawainiyar nPDP ta sa Kwankwaso sun fice sun fara harin hada-kai da sauran Jam’iyyu
Ta tabbata dai cewa tattaunawar ‘Yan nPDP da Jam’iyyar APC mai mulki yana cin lokaci don haka wasu daga cikin manyan ‘Yan nPDP su ka yanke shawaran tattarawa su bar APC gaba daya su koma Jam’iyyar PDP inda su ka fito.
Ganin irin tafiyar hawainiyar da ake yi tsakanin ‘Yan nPDP karkashin shugabancin Alhaji Kawu Baraje, wasu daga cikin ‘Yan Jam’iyyar APC mai mulki sun kuma bangarewa a makon nan sun kafa wata kungiya mai suna ‘Reformed APC’.
Mun samu labari daga This Day cewa Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da wasu manyan ‘Yan Majalisar kasar sun fice daga Kungiyar nPDP ganin maganar su Abubakar Kawu Baraje ta ki bullewa ga ko ina.
KU KARANTA: Babu abin da zai hana mu barin Jam’iyyar APC – Shehu Sani
Shugaban Tafiyar na Kwankwasiyya Rabiu Kwankwaso da wasu da ke da irin ra’ayin sa sun balle daga nPDP ne saboda ganin yadda lokaci ke tafiya ba su kuma iya shiga wata yarjejeniya da Jam’iyyar PDP da sauran Jam’iyyun adawar kasar ba.
Tattaunawar da Kawu Baraje da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ke yi da APC ta sa ‘Yan nPDP din su ka gaza samun matsaya kamar yadda mu ka samu labari. Shi dai Rabiu Kwankwaso da mutanen sa za su bar APC ne a Ranar Juma’a.
Kwankwaso za su zauna da kananan Jam’iyyu irin su SDP domin shiga wata yarjejeniya ta musamman da PDP. Zuwa karshen makon nan dai Jama’a za su ji idan Kwankwaso da Magoya bayan sa su ka sa gaba ganin cewa zaben 2019 ya kunno kai.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng