Sule Lamido ya kayar da gwamnatin jihar Jigawa a kotu
Babbar Kotun Jihar Jigawa dake garin Dutse, ta salami shari’ar da ake yi tsakanin tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido da Gwamnatin Jihar.
Gwamnatin Jigawa ce ta yi karar Sule a kotu bayan ta zarge shi da tunzura jama’a su tayar da zaune tsaye, bata suna da kuma barazana ga zaman lafiyar jihar a shekarar da ta gabata.
Tun a baya dai a Kotun Majistare ta garin Dutse ce, aka fara wannan shari’ar, inda bayan lauya Ruba ya kalubalanci kotun, a kan rashin hujja akan tuhumar da akeyiwa wanda ya ke karewa, inda bayan an dauki lokaci ana shari’a, Ruba ya daukaka kara zuwa Babbar Kotun garin Dutse.
A hukuncin da alkalan kotun uku suka zartas, Mai Shari’a Ahmed Gumel, Umar Sadiq da Abdulmumin Suleiman, duk sun yi watsi da caje-caje da gwamnatin jihar Jigawa ke yiwa Sule Lamido.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai tafi kasar Mauritania gobe
Kakakin gwamnatin jihar Jigawa, Bello Zaki, ya ce ba za a daukaka kara ba.
A halin da ake ciki, Sule Lamido ya kasance daya daga cikin masu neman kujerar shugabancin kasa a 2019 karkashin lemar jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku bide mu a shafukanmu na kafofin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.co
Asali: Legit.ng