Atiku da Kwankwaso sun yi ganawar sirri a Abuja

Atiku da Kwankwaso sun yi ganawar sirri a Abuja

Rahotanni sun kawo cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata a karkashin jam’iyyar APC Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara ga tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar.

Kwankwaso ya ziyarci Atiku ne a gidansa da ke babban birnin tarayya, Abuja inda suka yi ganawar sirri.

Idan baza ku manta ba, Kwankwaso bai samu halartar babban taron jam’iyyar APC da aka yi a karshen makon dfa ya gabata ba, sannan kuma daga bisani aka gan shi a gidan Atiku, inda suka yi wata ganawar sirri.

Atiku da Kwankwaso sun yi ganawar sirri a Abuja

Atiku da Kwankwaso sun yi ganawar sirri a Abuja

Kwankwaso ya bayyana dalilin da ya hana shi halartar gangamin taron da cewa shi da magoya bayansa sun yanke shawarar kauracewa taron don kaucewa aukuwar hargitsi a harabar zaben.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun hallaka daliban jami’a 2 sannan sun sace 1 a jihar Katsina

Shi dai Atiku yana cikin manyan wadanda ake tunani za su yi wa Jam’iyyar PDP takara a zaben shugaban kasa mai a 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel