Yan sanda sun damke masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da makami 21

Yan sanda sun damke masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da makami 21

- Dubun wasu masu laifi ta ciki, sun shiga hannun jami'an 'yan sanda

- An samu muggan makami da motoci a tare dasu bayan artun da yayi sanadiyyar mutuwar biyu dag cikinsu

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Benue ta samu nasarar kame wadansu da ake zargin suna da hannu a cikin muggan laifukan da suka hada da fashi da makami da garkuwa da mutane da kuma aiyukan ‘yan kungiyar asiri a luguna da sakon fadin jihar.

Yan sanda sun damke masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da makami 21
Yan sanda sun damke masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da makami 21

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Fatai Owoseni ne ya shaidawa maneman labarai a Makurdi a babban birnin jihar Makurdi.

Ya ce sun samu nasarar kame bata garin ne a cikin makonni biyo da suka gabata, kuma hudud aga ciki ana zarginsu ne da fashi, wasu hudun kuma ana zarginsu ne da yin garkuwa da mutane yayin da ragowar 13 kuma ake tuhumarsu da zamtowa ‘yan kungiyar asiri, sai kuma wasu biyu da suka mutu yayin musayar wuta da jami’an ‘yan sandan.

KU KARANTA: Fashin Offa: Hukumar 'Yan sanda ta sake cafke wasu da ake zargi a jihohin Kogi da Oyo tare da Muggan Makamai

Owoseni ya lissafa cewa sun samu nasarar kwato makamai daga wurin wadanda ake zargin da suka hada da ; manyan bindigu da kuma harsasai da wata karamar bidiga kirar Pistol guda daya tare da kakin sojoji da kuma motoci guda uku.

Kwamishinan ya kuma kara da cewa, rundunar ‘yan sanda ta jihar ta samar isassun jami’anta a wuraren shagulgula domin tabbatar da anyi bukukuwan Sallah lafiya, sannan ya roke mutane da su kai rahotan duk wani abu da basu yarda da shi ba ga jami’an tsaro mafi kusa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel