‘Yan biyu kyautar Allah: Kwararrun Likitocin Najeriya sun samu nasarar raba wasu ‘yan biyu da aka haifa tare
- Rabo daga Allah, ya baiwa wata mata kyautar haihuwar 'yan biyu
- Bayan likitoci sun taimake ta ta haihu, sai jariran suka zo a manne
- Bayan wasu watanni yanzu haka likitocin sun sake yiwa jariran tiyata sun raba su kuma aiki yayai kyau
Murna baki har kunne ga iyayen wasu ‘yan biyu da aka haifa a manne da juna, sakamakon samun nasarar raba su da likitoci su kayi ta hanyar tiyata a babbar cibiyar kula da lafiya da tarayya dake Yola.
Babban likitan da ya samu nasarar jagorantar raba jariran masu suna Fatima da Maryam mai suna Farfesa Auwal Mohammed Abubakar, ya bayyana jin dadinsa da godiya ga Allah da kuma abokan aikinsa bisa nasarar da suka samu a aikin.
“Suna cigaba da girma kamar yadda ya kamata jariran tun bayan tiyatar, don haka babu bukatar cigaba da rike su” Inji Farfesan.
Koda aka tambaye shi nawa ne kudin aikin da iyayen jariran suka biya, Farfesa Auwal cewa yayi, tun bayan da muka fuskanci iyalan ba su da karfi, kawai sai muka dauke musu dukkanin wani caji da ya kamata ayi musu, a takaice komai kyauta mu kayi musu.
Yanzu haka dai har an sallami mahaifan jariran masu suna Mohammed Ramat da matarsa Kellu, kuma sun koma garinsu Maiduguri. Kuma hukumar asibitin ce ta yi musu goma ta arziki yayin komawar tasu gida ranar Asabar din da ta gabata.
KU KARANTA: Haihuwa ba tayi rana ba: An damke wani matashi da ya antayawa mahaifiyarsa ruwan zafi
Kimanin watanni biyu da suka gabata ne aka karbi haihuwar ‘yan biyun shima ta hanyar tiyata a babban asibitin koyarwa na Maiduguri ranar 14 ga watan Mayu, tun sannan ne aka cigaba da rike su a asibitin.
Ana ta jawabinta mahaifiyar ‘yan biyun Kellu Adam, bayyana godiyarta tayi ga Allah da ya sanya aikin ya samu nasara, sannan ta godewa Farfesa Auwal da abokan aikinsa da kuma ragowar ma’aikatan cibiyar kula da lafiyar ta Yola, da ma duk sauran wadanda suka taimaka wajen nasarar aikin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng