Rikicin Makiyaya: An kashe mutane biyu tare da kai hari gidan Manjo-Janar Malu a jihar Plateau

Rikicin Makiyaya: An kashe mutane biyu tare da kai hari gidan Manjo-Janar Malu a jihar Plateau

- Tsugunno bai kare kan batun matsalar rashin tsaro da kuma rikicin makiyaya

- Yanzu haka wasu mutane biyu sun rasa rayukansu a wani rikicin a Plateau

- Amma sai dai yunkurin wasu 'yan bindiga ya gamu da cikas bayan da su kayi artabu da jaruman Sojoji

A kalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu a wani hari da Makiyaya suka kai akan wasu yan kabilar Irigwe dake karamar hukumar Bassa a jihar Plateau.

Rikicin Makiyaya: An kashe mutane biyu tare da kai hari gidan Manjo-Janar Malu a jihar Plateau
Rikicin Makiyaya: An kashe mutane biyu tare da kai hari gidan Manjo-Janar Malu a jihar Plateau

Jaridar Punch ta tattara bayanai cewa al'amarin ya faru ne da misalin karfe 7:40pm na daren ranar lahadi, wanda lamarin ya ritsa da su, suna kan hanyarsu ta komawa gida ne akan babur din hawa ne.

KU KARANTA: Sai a nemi Jannareto: Ku shiryawa fuskantar rashin samun wuta a lokacin Damuna – Fashola

Mai magana da yawun hukumar yan sanda ta jihar plateau Mathias Tyopev, wanda mataimakin Sufiritanda yan sanda ne ya tabbatar da aukuwar lamari a ranar litinin idan ya ce yanzu haka hukumar tasu tana kan bincke domin samun wasu bayanai.

Har wa yau, a ranar litinin ne wasu ya. Bindiga suka shiga gidan tsohon manjo-janar John Malu wanda dan uwa ne ga tsohon kakakin shugaban sojin kasar nan Janar Victor Malu. Maharban sun far masa a gidansa wanda ba shi da nisa da madakatar bincike ta kan hanya ta hadin guiwar jami'an tsaro. Sojojin dake gadinsa a gidansa sun far wa da maharban inda aka dauki lokaci ana bata-takashi.

Rikicin Makiyaya: An kashe mutane biyu tare da kai hari gidan Manjo-Janar Malu a jihar Plateau
Rikicin Makiyaya: An kashe mutane biyu tare da kai hari gidan Manjo-Janar Malu a jihar Plateau

Sai dai yan bindigar basu yi nasara ba domin sojojin dake gidan sun kora su, bayan da komai ya lafa manema labarai sun tambayi wani soja dan jin ta bakinsa inda yace "Tabbas yan bindigar sun shigo cikin gida domin kawu hari ga mai gida sai dai mun dakile manufar tasu, kuma yanzu haka maigida yana lafiyarsa kalau".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel