Anyi wani mummunan hadarin mota a jihar Jigawa

Anyi wani mummunan hadarin mota a jihar Jigawa

Mutane biyu sun rasa rayukan su, inda wasu suka samu munanan raunuka, a yayinda wani mummuman hadarin mota ya auku akan hanyar Kano zuwa karamar hukumar Birnin Kudu dake cikin jihar Jigawa

Anyi wani mummunan hadarin mota a jihar Jigawa
Anyi wani mummunan hadarin mota a jihar Jigawa

Mutane biyu sun rasa rayukan su, inda wasu suka samu munanan raunuka, a yayinda wani mummuman hadarin mota ya auku akan hanyar Kano zuwa karamar hukumar Birnin Kudu dake cikin jihar Jigawa. Shugaban hukumar kiyaye hadura na jihar Jigawa, Angus Ibezim, shine ya sanar da hakan a lokacin da yake magana da manema labarai a jiya.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari na tsoron zaben 2019

Ya ce hadarin ya faru ne sanadiyyar fashewar taya da wata motar kasuwa tayi mai kirar Golf Volkswagen.

Ibezim ya tabbatar da cewar hadarin ya faru ne a jiya da misalin karfe 6 da minti 55 na safe, inda ya tabbatar da cewar an kai wadanda suka ji raunin babban asibitin tarayya dake karamar hukumar ta Birnin Kudu.

Shugaban hukumar kiyaye haduran yace motar da ya kamata ace ta dauki mutane biyar, amma sai aka loda mata mutane 10.

A karshe yace an samu kusan sama da naira 240,000 a cikin kayan wadanda abin ya shafa, inda aka mika kudaden ga iyalan su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: