Da dumin sa: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade na shugabannin hukumomi 4

Da dumin sa: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade na shugabannin hukumomi 4

Labarin da muke samu da dumin sa yanzu haka na nuni ne da cewa shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya sace amincewa da nadin wasu mutane hudu da za su shugabanci hukumomin gwamnatin tarayya a matakai daban-daban.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin Sakataren dindindin na ofishin babban Sakataren gwamnatin tarayya mai suna Olusegun A. Adekunle.

Da dumin sa: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade na shugabannin hukumomi 4
Da dumin sa: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade na shugabannin hukumomi 4

KU KARANTA: Baitulmalin Najeriya ta kai $47 biliyan - Buhari

Legit.ng ta samu dai cewa wadanda aka nada din shun hada da Dakta Anasa Ahmad Sabir, shugaban asibitin koyarwa ta tunawa da Usman Danfodio (UDUTH), Sokoto; Dakta. Theresa Obumneme Okoli, a matsayin shugaban kwalejin koyon malanta ta jihar Anambra State.

Sauran sune Dakta Emmanuel Ikenyiri, a matsayin shugaba da kuma Dakta Pius Olakunle Osunyikanmi, a matsayin Darakta a hukumar nan ta bayar da gaji ta Directorate of Technical Aid Corps.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel