An tsaurara matakan tsaro yayin gurfanar tsohon gwamnan Jos a kotu

An tsaurara matakan tsaro yayin gurfanar tsohon gwamnan Jos a kotu

- Yau hukumar EFCC zata gurfanar da tsohon gwamnan jihar Plateau duk da cewa yana fama rashin lafiya

- Sai dai kuma wasu Mutane suna ta zanga-zangar nuna goyon bayansa

A yau aka gurfanar da tsohon gwamnan jihar Plateau Jonah David Jang gaban babbar kotu a jihar da misalin karfe 9:28am na safe.

Gwamnan dai an kawo shi harabar kotun ne cikin Mota kirar Toyota Hiace bisa rakiyar jami’an hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC da kuma jami’an ‘yan sanda.

An tsaurara matakan tsaro yayin gurfanar tsohon gwamnan Jos a koto
An tsaurara matakan tsaro yayin gurfanar tsohon gwamnan Jos a koto

Tsohon gwamnan an gurfanar da shi ne gaban alkalin babbar kotun mai shari’a Daniel Longji bisa zarginsa da laifuka har 12 da suke da alaka da cin hanci da rashawa da kuma barnatar da dukiyar al’umma da suka kai har Naira biliyan N6.3b bayan ya sauka daga mukamin gwamnan jihar ta Plateau.

KU KARANTA: Ta faru ta kare: Buhari ya tona asirin dalilin da ya sanya aka yi masa juyin mulki a 1985

Majiyar Daily Trust ta rawaito cewa an tsaurara matakan tsaro a ko’ina a farfajiyar kotun da wajenta. kuma an hana masu gudanar da zanga-zangar goyon bayan gwamna Jang din shiga farfajiyar kotun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng