Ji ku qaru: Banbanci tsakanin Gurguzu da Jari Hujja

Ji ku qaru: Banbanci tsakanin Gurguzu da Jari Hujja

- Jari Hujja shi ake kira Capitalism a turance, Gurguzu shine Communism

- Kasashen Yamma sun fi son Jari Hujja, Gabas kuma sunfi son Gurguzu

- Kowanne tsari yana da alfanu da aibi, sai dai ba safai ake sa'a ba

Ji ku qaru: Banbanci tsakanin Gurguzu da Jari Hujja
Ji ku qaru: Banbanci tsakanin Gurguzu da Jari Hujja

An gwabza yaki sosai, an mummutu, kan tsarin tattalin arziki da ake gani yafi dacewa da jama'a a tarihin duniya na wancan qarni, inda shi ya mamaye kusan dukkan yake-yake da juyin-juya hali da aka sha fama dasu a karni na 20.

Kasashen Yamma, inda daga nan ne aka sami Karl Max, bayahuden Jamus, da Thomas Engles, na Ingila, suka zayyana yadda ya kamata kasashe su zamo ta karkashin Gurguzu, sun ki amsar wannan tsari.

Amma kasashen gabas kamar su Rasha, USSR ta wancan lokacin, China, Mongolia, Vietnam, Laos, Venezuela da Cuba su suka rungumi tsarin gurguzu gadan-gadan.

DUBA WANNAN: An jefe wata mata har lahira

Shi dai Gurguzu, tsari ne dake ganin ana cin zalin talakka, a karkashin Jari Hujja, inda masu kudi kan tare duk dukiya su saki kadan ga ma'aikata ta hanyar masana'anntu ko gonaki, arziki nasu riba tasu.

Shi Gurguzu, so yake ace babu wani hamshakin mai kudi, babu kuma mai mallakar uwar dukiya, ko ta gado ko ta sata ko ta gwamnati, tsari ne dake son kowa ya tsaya daidai gwargwado, babu bakin talauci, kowa abinci ya ishe shi, amma fa babu wata walwala.

Jari Hujja kuwa, so yake kowanne mutum, ya iya mallakar iya arzikin da ya iya nema, ko ta halas ko ta haram, ya rike shi-shi kadai, sai yaga dama ya bayar.

Jari Hujja kan baiwa jama'a damar tunanin hanyoyin neman kudi, shi kuwa gurguzu ko kayi tunanin ka samo, gwamnati zata kwace ta raba wa talakawa.

A jari hujja mai aski, ko manomi kan iya ajje ciniki ko girbensa shi da iyalinsa su mora, amma a gurguzu, kowa gwamnati yake wa aiki, ko hukuma, a ko yaushe za'a tara duk kudi ko kayan girbe da aka tara a raba dai dai ga kowa.

Wannan kan kashe wa wasu jiki, tunda don me zanyi aiki tuquru, in noma buhu dari, bayan ukku kawai za'a bani a karshe? Don me zan wahala? Wannan ya sanya kasashen gurguzu suka durkushe, kowa jira yake ya bada kadan a bashi da yawa, babu wani karsashi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng